Allah shi kyauta: Mai gadi dan shekara 65 ya keta haddin diyarshi

Allah shi kyauta: Mai gadi dan shekara 65 ya keta haddin diyarshi

- An gurfanar da wani mai gadi dan shekara 65 mai suna Yisa Showunmi da ya keta haddin kanan yara guda hudu ciki hadda diyarshi ta cikinshi a gaban kotu

- Dan sanda mai gabatar da kara ya bayyana ma kotun cewa wanda ake tuhuma da laifin ya aikata laifin ne a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2019

- Kotun ta dage sauraron karar zuwa 7 ga watan Agusta na 2019 bayan da ta bada wanda ake kara beli

A jiya Laraba, 10 ga watan Yuli 2019 aka gurfanar da wani mai gadi dan shekara 65 mai suna Yisa Showunmi da ya keta haddin kanan yara guda hudu ciki hadda diyarshi ta cikinshi a gaban kotun majistire a jihar Legas.

Dan sanda mai gabatar da kara, ASP Ezekiel Ayorinde ya bayyana ma kotun cewa wanda ake tuhuma da laifin ya aikata laifin ne a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2019. Ayorinde ya bayyana ma kotu cewa yan matan hudu dukkansu yan shekaru 16 ne.

Kotun ta magistire da mai shari’a Bola Osunsanmi ke gudanarwa ba ta tambayi wanda ake kara ko ya aikata laifin ba, illa dai ta bayar da shi beli akan kudi Naira 200,000 da kuma mutane biyu da za su tsaya mashi.

KARANTA WANNAN: Yadda ’ya’yana maza 3 suka makance suna samari – Inji wata uwa

Mai shari’ar ta bayyana cewa mutane biyun da za su tsaya ma wanda ake kara sai sun tabbatar wa da kotun cewa suna da aikin yi kuma sai sun nuna takardar biyan haraji ga gwamnatin Legas na shekara biyu.

Mai shari’a Bola ta umurci yan sanda masu gabatar da kara da su gurza irin takardar karar su tura ga ma’aikatar shari’a don su bayar da shawara. Alkaliyar ta dage sauraron karar zuwa 7 ga watan Agusta na 2019.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel