Da dumi-dumi: Yan Shi'a sun sake arangama da 'Yan sanda a Abuja, an kama mutum biyar

Da dumi-dumi: Yan Shi'a sun sake arangama da 'Yan sanda a Abuja, an kama mutum biyar

Mambobin Kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) da akafi sani da Shi'a sun sake arangama da jami'an 'Yan sanda a Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da ke Abuja a yau Alhamis 11 ga watan Yuli.

'Yan sandan sun rika harbe bindiga da borkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zangar yayin da aka kama mutane biyar cikin masu zanga-zangar.

The Punch ta ruwaito cewa arangamar ya haifar da tashin hankali inda ma'aikata da masu ababen hawa suka rika tserewa domin kada rikicin ya ritsa da su.

DUBA WANNAN: An kama wasu mata 4 dumu-dumu suna madigo a Kwallejin Kimiyya a Kebbi

'Yan kungiyar ta IMN sun sake haduwa a wani mattatara inda za su cigaba da gudanar da zanga-zangar su.

A ranar Talata ne 'yan Shi'an su kayi kutse cikin harabar Majalisar Wakilai na Tarayya inda suka harbe 'yan sanda biyu tare da kone motocci uku da lalata wasu kayayaki.

An kama mutane 40 cikin masu zanga-zangar na ranar Talata inda tuni an gurfanar da su gaban kuliya domin hukunta su.

A baya, Legit.ng ta rahoto cewa 'Yan Majalisar Wakilan Tarayya sun shawarci Gwamnatin Tarayya tayi biyaya ga umurnin kotu na bayar da belin Shugaban IMN, Sheikh IbrahimEl Zakzaky da ake tsare da shi tun 2015.

'Yan Majalisar sun gargadi gwamnati cewa rashin sakinEl Zakzaky zai iya haifar da wata matsala mai kama da na Boko Haram.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel