Matasa sun fi dattawa kwazon bayar da cin hanci - Rahoto

Matasa sun fi dattawa kwazon bayar da cin hanci - Rahoto

Rahoton da aka wallafa a mujallar sa ido kan rashawa ta Global Corruption Barometer (GCB) – Africa da Transaparency International ta fitar karo na 10 tare da hadin gwiwan Afrobarometer ya bayyana cewa fiye da rabin mutanen kasashen Afirka 35 suna ganin rashawa yana kara kazanta ne a kasashensu.

Kashi 55 cikin 100 na al'umma suna ganin gwamnatocin su ba su aikata abinda ya dace wurin yaki da rashawa.

Bincike mafi girma da aka gudanar kan rashawa a kasashen Afirka ya tambayi mutane 47,000 a kasashe 35 ra'ayinsu kan rashawa da cin hanci a kasashensu.

DUBA WANNAN: An kama wasu mata 4 dumu-dumu suna madigo a Kwallejin Kimiyya a Kebbi

Binciken ya nuna cewa mutum 1 cikin 4 da ya bayar da cin hanci a ma'aikatan gwamnati a shekarar da ta gabata. Hakan na nufin kimanin mutane miliyan 130 ne suka bayar da cin hanci a shekarar da ta gabata.

Rahoton ya kuma nuna cewa talakawa ne suka fi shan wahala sakamakon rashawar dubba da cewa talakawan na biyan cin hanci da ta rubanya wanda masu arziki ke biya.

Binciken ya kuma nuna matasa sun fi bayar da rashawa fiye da mutane masu shekaru fiye da 55.

"Cin hanci yana kawo cikas ga cigaban tattalin arziki, siyasa da walwalar mutanen Afrika. Shine babban abinda ke hana cigaban tattalin arziki da 'yan cin al'umma na bayyana ra'ayoyinsu," a cewar Patricia Moreira, Direktan Transparency International.

Binciken ya kuma nuna cewa mutane na ganin 'yan sanda ne suka fi tafka cin hanci inda kashi 47 cikin 100 suke ganin mafi yawancin ko dukkan 'yan sanda na da hannu cikin karbar cin hanci da rashawa. Masu biye musu kuma sune ma'aikatan gwamnati da 'yan majalisa da kashi 39 cikin 100 da kashi 36 cikin 100.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel