Tirkashi: Yadda aka kusa binne Muhammad da ranshi bayan asibiti sun bada tabbacin cewa ya mutu

Tirkashi: Yadda aka kusa binne Muhammad da ranshi bayan asibiti sun bada tabbacin cewa ya mutu

- Wani matashi dan shekara 20 a duniya ya sha dakyar yayin da aka yi kokarin binne shi da ranshi

- Hakan ya biyo bayan wani hatsarin da ya ritsa da matashin, inda aka garzaya dashi asibiti domin duba lafiyarsa

- Daga baya malaman asibitin sun bayyanawa iyayensa cewa ya mutu, bayan iyayen sun nuna musu cewa baza su iya biyan kudin maganin shi ba

Wani matashi dan shekara 20 da ya gamu da wani mummunan hatsari, an yi gaggawar kai shi wani asibiti mafi kusa a ranar 21 ga watan Yuni, 2019.

Daga baya an fara shirin yin jana'izar matashin bayan asibitin da aka kai shi sun bayyana cewa ya mutu.

Wani rahoto da jaridar Indiya ta Hindustan ta ruwaito, ta bayyana cewa Mohammad Furqan, wanda yake dan jihar Uttar Pradesh dake kasar Indiya, asibitin da aka kai shi sun bayyana cewa ya mutu, inda suka bai wa iyayen shi gawarshi domin a binne shi, bayan iyayen sun bayyanawa asibitin cewa basu da kudin da zasu iya biya ayi masa magani.

KU KARANTA: To fah: Ina son Sa'eed wanda matarsa ta cakawa wuka - Inji Ummi Abdullahi Kaduna

A lokacin da ake shirin binne shi, iyayen Furqan sun gano cewa wani bangare na jikinshi yana yin motsi kadan-kadan, cikin gaggawa suka kara komawa dashi asibiti, likitocin sun bayyana cewa yana numfashi, ma'ana da ranshi.

A lokacin da Furqan ke fama da kanshi a asibitin, shugaban hukumar lafiya na yankin, Narendra Agarwal ya bayyana cewa dole sai an dauki mataki akan abinda asibitin suka yi akan Furqan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel