Sunayen Ministoci: Buhari da shugabannin majalisar Tarayya za su gana a fadar shugaban kasa

Sunayen Ministoci: Buhari da shugabannin majalisar Tarayya za su gana a fadar shugaban kasa

A yayin da ake ci gaba da kirdadon gabatar da sunayen ministoci zuwa ga majalisar dattawa domin tantantacewa tare da tabbatar wa, shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Alhamis 11, ga watan Yuli zai karbi bakuncin shugabannin majalisar Tarayya a fadar sa ta Villa.

Cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 10 ga watan Yuli tare da sa hannun shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, za a gudanar da wannan liyafa a tsakanin masu rike madafan iko na kasar nan da misalin karfe 8.00 na Yammacin yau Alhamis a fadar Villa.

Wasikar da manema labarai suka bayar shaidar rubutun ta, ta bayyana cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan, shi ne zai jagoranci tawagar kusoshin majalisar Tarayya zuwa wajen ganawar da zata gudana a tsakanin su tare da shugaba Buhari a fadar sa.

Kazalika, wasikar da ta fito daga fadar shugaban kasa ta yi karin haske na bayyana yadda tuni shugaba Buhari ya aike da sunayen zababbun ministoci 15 zuwa ga mashawartan sa domin tantancewa.

KARANTA KUMA: Abuja da jihohi 30 da suka tarawa Najeriya bashin N24.9tr - DMO

Cikin wani rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito, shugaban kasa Buhari ya tabbatar da nadin mukamin Justice Tanko Muhammad, a matsayin alkalin alkalai na kasar nan bayan da hukumar shari'a ta kasa ta shawarce shi a kan aiwatar da hakan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel