Akwai alamun Fashola, Amaechi da Onu za su rike mukamansu

Akwai alamun Fashola, Amaechi da Onu za su rike mukamansu

-A lokacin da ake tsammanin fitar da sunayen mutanen da za a nada a matsayin ministoci, alamu na nuna cewa shugaba Buhari zai tafi da wasu tsofaffin ministocinshi

-Ana tunanin cewa sunan tsofaffin mimistocin na cikin sunayen da ake tsammanin fadar shugaban kasa ta tura ma shugaban majalisar dattawa a ranar 10 ga watan Yuli 2019

A lokacin da mutanen Najeriya ke zaman jiran sunayen mutanen da shugaba Buhari zai nada a matsayin ministoci, alamu na nuna cewa shugaba Buhari zai tafi da wasu daga cikin tsofaffin ministocinsa.

Ana zaton cewa sunayen tsofaffin ministocin na cikin sunayen da ake tunanin shugaba Buhari ya mika ga shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan a jiya Laraba 10 ga watan Yuli 2019.

Mutanen da ake tunanin da su cikin sunayen da aka tura sun hada da tsohon ministan shari’a Abubakar Malami (SAN), Adamu Adamu, Hadi Sirika, Zainab Ahmed, Aisha Abubakar, Lai Mohammed, Babatunde Fashola, Rotimi Amaechi, Musa Bello, Suleiman Adamu Kazaure, Ogbonnaya Onu, Solomon Dalung da sauransu.

Legit.ng ta ruwaito wata majiya daga fadar shugaban kasa na cewa “Ba wai za a canza su gaba daya ba kamar yadda kuke tsammani. Abinda shugaban kasa yayi alkawari shine za ya bar mahimman abubuwa a zangon mulkinshi na biyu.”

KARANTA WANNAN: To fah: Ina son Sa'eed wanda matarsa ta cakawa wuka - Inji Ummi Abdullahi Kaduna

Wata majiyar kuma cewa tayi “Ina tunanin an riga an tura sunayen ga shugaban majalisar dattawa, amma sun ce kada a bayyana sunayen sai ranar Alhamis.

Legit.ng ta ruwaito cewa shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya bayyana cewa za su karbi sunayen ministoci daga wajen shugaban kasa kafin ranar Juma’a 12 ga watan Yuli 2019.

Lawan ya bayyana hakan a ranar Laraba 10 ga watan Yuli 2019 a lokacin da yake sauraren jan hankali da sanata mai wakiltar arewa maso gabashin Akwa Ibom, Abert Bessy Akpan yayi, wanda ya bayyana damuwarshi akan jan jiki da fadar shugaban kasa ke yi wajen tura sunayen ministoci.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel