Da zafi-zafi: Buhari ya gabatar da sunan Justis Muhammed a matsayin tabbataccen Shugaban alkalan Najeriya

Da zafi-zafi: Buhari ya gabatar da sunan Justis Muhammed a matsayin tabbataccen Shugaban alkalan Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattawa da ta tabbatar da mukaddashin Shugaban alkalan Najeriya, Ibrahim Tanko Muhammad a matsayin tabbataccen Shugaban alkalan kasar.

Buhari a cikin wasikar wanda Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanta a zauren majalisa a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli yace bukatar ya biyo bayan shawarar da kungiyar alkalan Najeriya ta bayar cewa a tabbatar da mukaddashin CJN din.

Majalisar Alkalai Ta Najeriya (NJC) ta bukaci Shugaba Muhamamdu Buhari ya tabbatar da Alkalin Alkalai na wucin gadi, Justice Tanko Muhammad a matsayin tabbatacen Alkalin Alkalai na kasa.

An cimma wannan matsayar ne yayin wata taron gaggawa da majalisar ta gudanar karkashin jagorancin tsohon Shugaban Kotun Daukaka Kara na Kasa, Justice Umaru Abdullahi.

KU KARANTA KUMA: Zanga-zangar yan shi’a: Majalisar dattawa ta dauki mataki, ta tsaurara matakan tsaro a harabar majalisar

A cikin jawabin da Direktan Yada Labarai na NJC, Soji Oye ya fitar a ranar Laraba, 10 ga watan Yuli ya ce an cimma matsayar ne sakamakon rahoton da kwamitin da aka nada don tantance sabon alkalin alkalai na kasa ta gabatar da rahoton ta.

Muhammed ya kasance mukaddashin Shugaban alkalan kasar tun daga ranar 25 ga watan Janairu na wannan shekarar bayan dakatar da tsohon Shugaban alkalan, Walter Onnoghen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel