Abuja da jihohi 30 da suka tarawa Najeriya bashin N24.9tr - DMO

Abuja da jihohi 30 da suka tarawa Najeriya bashin N24.9tr - DMO

Cibiyar kula da bashi ta kasa, DMO (Debt Management Office), cikin rahoton da ta fitar a ranar Larabar da ta gabata ta bayyana cewa, a halin yanzu bashin da ya yiwa kasar nan katutu ya kai Naira tiriliyan 24.947, kimanin Dalar Amurka Biliyan 81.274.

Sabanin rahoton da cibiyar DMO ta fitar a ranar 31 ga watan Dasumban 2018, nauyin bashin dake kan gwamnatin kasar nan ya tumfaya daga dalar Amurka biliyan 79.437 inda a yanzu aka samu doriyar kaso 2.30 cikin 100.

Daga yadda kididdigar DMO ta bayyana, gwamnatin Tarayya da kuma wasu jihohi 30 na kasar nan ke kan sahu na gaba ta fuskar alhakin wannan nauyin bashi da ya kara a kan na baya wajen yiwa kasar nan katutu.

Dalla Dalla ga yadda nauyin bashin ya kasance a tsakanin jihohi 36 da kuma babban birnin kasar nan na Tarayya:

1. Abia N62,849,599,630.68;

2. Adamawa (N97,153,965,072.71);

3. Akwa Ibom (N199,768,698,811.90);

4. Anambra (N33,490,668,536.72);

5. Bauchi (N93,319,627,053.30);

6. Bayelsa (N133,339,375,587.91);

7. Benuwai (N96,905,502,591.02);

8. Borno (N78,259,334,907.05);

9. Cross-River (N167,252,341,140.66);

10. Delta (N223,442,257,101.69);

11. Ebonyi (N55,597,352,310.28);

12. Edo (N86,367,405,983.76);

13. Ekiti (N118,011,414,814.34);

14. Enugu (N55,882,997,585.01);

15. Gombe (N76,894,514,835.51);

16. Imo (N97,851,149,167.90);

17. Jigawa (N38,227,157,463.84);

18. Kaduna (N93,203,947,964.61);

19. Kano (N121,305,201,113.25);

20. Katsina (N67,098,008,669.65);

21. Kebbi (N67,037,456,840.31);

22. Kogi (N96,677,066,212.09);

23. Kwara (N59,576,712,572.23);

24. Lagos (N542,231,174,761.82);

25. Nasarawa (N89,953,619,684.92);

26. Niger (N43,414,653,538.03);

27. Ogun (N97,090,119,332.73);

28. Ondo (N56,959,970,712.20);

29. Osun (N147,702,865,382.96);

30. Oyo (N94,140,261,739.96);

31. Filato (N98,585,866,556.33);

32. Rivers (N225,592,469,150.22);

33. Sokoto (N36,571,742,397.44);

34. Taraba (N68,569,699,976.43);

35. Yobe (N26,990,637,417.62);

36. Zamfara (N61,950,819,816.58);

37. Abuja (N163,518,714,908).

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel