Zanga-zangar yan shi’a: Majalisar dattawa ta dauki mataki, ta tsaurara matakan tsaro a harabar majalisar

Zanga-zangar yan shi’a: Majalisar dattawa ta dauki mataki, ta tsaurara matakan tsaro a harabar majalisar

- Biyo bayan zanga-zangar da yan shi’a suka yi, majalisar dattawa tayi kira ga tsaurara matakan tsaro a kewayen harabar majalisar dokokin kasar

- Tuni Shugaban Majalisar dattawan ya fara tattaunawa da hukumomin tsaron da ke binciken lamarin

- Majalisar ta kuma bukaci dukkanin hukumomin doka da su tashi tsaye cikin gaggawa domin kamo wadanda suka aiwatar da mumunan aikin

Biyo bayan zanga-zangar da mambobin kungiyar shi’a suka yi wanda ya kai ga zubar da jini, majalisar dattawa a ranar Laraba, 10 ga watan Yuli tayi kira ga tsaurara matakan tsaro a kewayen majalisar dokokin tarayya.

Shugaban kwamitin wucin gadi na majalisar dokoki kan harkokin labarai da jama’a, Sanata Adedayo (APC-Ekiti), ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa tuni Shugaban Majalisar dattawan ya fara tattaunawa da hukumomin tsaron da ke binciken lamarin.

KU KARANTA KUMA: Idan kunne ya ji: Kada ku dauki miyagun kwayoyi zuwa kasa mai tsarki – Dabiri-Erewa ta gargadi mahajjata

Adeyeye ya yaba ma jami’an tsaro da suka kula da lamarin zanga-zangar kan yadda suka riki masu zanga-zangar.

Majalisar ta kuma bukaci dukkanin hukumomin doka da su tashi tsaye cikin gaggawa domin kamo wadanda suka aiwatar da mumunan aikin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel