PDP za ta binciki dalilin da ya sanya wasu yan jam’iyyar suka zabi Lawan da Gbajabiamila

PDP za ta binciki dalilin da ya sanya wasu yan jam’iyyar suka zabi Lawan da Gbajabiamila

- Jam’iyyar PDP ta kafa wani kwamiti da zai binciki yadda yan jam’iyyar suka gudanar da zaben shuwagabannin majalisa ta tara

- Tsohon sanata, Adolphus Wabara ne zai jagoranci kwamitin na mutum 10

- Kwamitin na da alhakin bayar da shawarwari akan hanyar da za a bi wajen hana sake bijirewa umurnin jam'iyyar

Jam’iyyar PDP ta kafa wani kwamiti da zai binciki yadda yan jam’iyyar suka gudanar da zaben shuwagabannin majalisa ta tara a lokacin da aka gudanar da zaben cikin watan Yuni.

Da yake kaddamar da kwamitin a Abuja, shugaban jam’iyyar Uche Secondus ya bayyana cewa kwamitin na da sati uku da za su gudanar da binciken.

Shugaban jam’iyyar wanda ya samu wakilcin mataimakin sakataren jam’iyyar na kasa (na Kudu), Yomi Akinwonmi, ya ce tsohon sanata, Adolphus Wabara ne zai jagoranci kwamitin na mutum 10.

Sauran mamabobin kwamitin sun hada da Wale Oladipo da zai aiki a matsayin sakataren kwamitin, Ben Obi, Yohanna Iliya, Ibrahim Mantu, Austin Opara, Stella Omu, Margret Icheen, Hassan Hayat, da Abdul Ningi.

Secondus ya bayyana cewa wannan hukuncin da jam’iyyar ta yanke alamu ne na dimukaradiyyar cikin gida inda ya kara da cewa “Wannan ne abu mai kyau da PDP ta ke da shi wanda sauran jam’iyyu basu da shi.”

“Wannan ne abun da ya kawo mu zuwa yanzu, saboda muna girmama dimukaradiyyar cikin gida. Muna magance matsaloli ta hanyar yin sulhu, ta hanyar tattaunawa, ta hanyar sauraren kowannen bangare. Wannan ne abunda ba zaka samu ba a sauran jam’iyyu na Najeriya.” a cewarshi

KARANTA WANNAN: Naira ta kusa zama labari: Za'a fara amfani da kudin ECO nan da shekara 1 - Ouattara

Secondus ya bayyana cewa aikin kwamitin shine su binciko dalilin da ya sanya yan majalisa na jam’iyyar suka ki bin umurnin da jam’iyyar ta yanke game da zaben shuwagabannin majalisa.

Ya kuma bayyana cewa kwamitin na da alhakin bayar da shawarwari akan hanyar da za a bi wajen hana sake afkuwar bijirewa umurnin jam'iyyar da kuma duba yadda za a kare ra’ayoyin jam’iyya a kowannen lokaci.

Shugaban jam’iyyar ya ba wa yan kwamitin shawara da su mika hannuwansu zuwa sauran yan jam’iyya hadda gwamnoni don ganin sun samu shawarwari masu kyau da za su ba jam’iyyar.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel