Buhari zai kaddamar da katafariyar asibiti a Abuja

Buhari zai kaddamar da katafariyar asibiti a Abuja

- Shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar da asibitin ido na gidauniyar Tulsi Chanrai a Abuja

- Shugaban gidauniyar Tulsi Chanrai ne ya bayyana haka, inda ya ce za a rinka yi ma talakawa ragin kashi 60% na kudin da za a ca je su

- Asibitin wanda ke anfani da sanannen tsarin kula da lafiyar ido irin na 'Aravind', na yin aiki da kwararrun yan Najeriya 30 da suka kammala ansar horo

A yau Alhamis, 11 ga watan Yuli 2019, shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar da asibitin ido na gidauniyar Tulsi Chanrai a Abuja.

Asibitin wanda ke anfani da sanannen tsarin kula da lafiyar ido irin na 'Aravind', na yin aiki da kwararrun yan Najeriya 30 da suka kammala ansar horo akan lafiyar ido a kasar India.

Da yake zantawa da yan jarida a Abuja, Jagdish Chanrai wanda shine ya kirkiri wannan gidauniya ta Tulsi Chanrai (TCF) ya bayyana cewa asibitin zai rinka yi ma talakawa ragin kashi 60% na kudin da za a ca je su, sa’annan kuma sauran mutane ma za a rinka yi masu ragi.

Chanrai ya bayyana cewa asibitin ya fara aiki ne tun cikin watan Janairun wannan shekarar kuma ya duba lafiyar idon mutane 6,400 kuma ya yima mutum 1000 aikin ido wanda cikinsu akwai talakawa 850 da aka yi masu aikin kyauta.

KARANTA WANNAN: Wannan rashin imani da mai yayi kama: Wani mutumi ya yiwa matarsa yankan rago a gaban 'ya'yansu saboda taqi yarda ya kwanta da ita

Chanrai ya bayyana cewa iyalan Chanrai ne suka kirkiri gidauniyar a shekarar 1992 kuma gidauniyar ta taimaki yan Najeriya miliyan 7.5 ta hanyoyi daban daban a jihohi 32 a fadin kasar nan

Wani majinyaci, Tertima Emmanuel ya bayyana cewa an yi mashi aikin cire yanar ido kuma an ca je shi kashi 10 kacal na kudin aikin da aka yi mashi.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel