Idan kunne ya ji: Kada ku dauki miyagun kwayoyi zuwa kasa mai tsarki – Dabiri-Erewa ta gargadi mahajjata

Idan kunne ya ji: Kada ku dauki miyagun kwayoyi zuwa kasa mai tsarki – Dabiri-Erewa ta gargadi mahajjata

Shugabar hukumar kula da yan Najeriya a kasashen waje (NIDCOM), Misis Abike Dabiri-Erewa, ta gargadi mahajjatan wannan shekarar da su gaje ma duk wani yunkuri na daukar miyagun kwayoyi zuwa kasa mai tsarki.

Da take Magana taron kaddamar da tashin alhazai, Misis Dabiri-Erewa ta tunatar dasu cewa dokar kasar Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa akan aikata hakan.

A wani jawabi daga Shugaban sashin labarai na NIDCOM, Mabdur-Rahaman Balogun, shugabar hukumar tace abun bakin ciki ne cewa har yanzu wasu yan Najeriya na fadawa cikin ragar dokar hukumar Saudiyya, duk da tarin gargadi da horarwa daa ake wa mahajjatan.

Ta tuna cewa an kama wasu yan Najeriya a hannu dauke da miyagun kwayoyi a yan shekarun da suka gabata sannan cewa har yanzu suna cikin jerin wadanda za a yanke wa hukuncin kisa a Saudiyya.

Shugabar NIDCOM din ta roki mahajjata da su guje ma abun kunya.

Misis Dabiri-Erewa ta kuma tunatar dasu cewa an haramta shiga da goro da maganin zazzabi da yawa a kasar Saudiyya.

Ta kuma yi gargadin cewa idan aka kama shi a tare da mutum, za a hukunta shi hukunci mai tsanani daidai da tsarin Saudiyya.

KU KARANTA KUMA: To fah: Ina son Sa'eed wanda matarsa ta cakawa wuka - Inji Ummi Abdullahi Kaduna

Daga karshe ta bayyana cewa gwamnatin tarayya, ta hukumar NAHCON da hukumomin jihohi daban-daban, ta samar da tsare-tsare kan yadda za a kula da lafiyar mahajjata idan bukatar hakan ta taso a Saudiyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel