Yan majalisa na bukatar a sanya gwagwarmayar 12 ga watan Yuni cikin manhajar karatun tarihi

Yan majalisa na bukatar a sanya gwagwarmayar 12 ga watan Yuni cikin manhajar karatun tarihi

- Majalisar wakilai ta yi kira ga ministirin ilimi ta gwamnatin tarayya da ta saka gwagwarmayar June 12 a cikin manhajar karatun tarihi

- Hakan ya biyo bayan amincewa da majalisar ta yi da wani kudirin da Olumide Osoba ya gabatar na a sanya labarin gwagwarmayar a cikin manhajar karatun tarihi a makarantun kasar nan

- Osoba ya bayyana cewa in har ba a sanya gwagwarmayar cikin manhajar karatun tarihi a makarantu ba, to kananan yara masu tasowa ba za su fahimci mahimmancin ranar ba

A jiya Laraba, 10 ga watan Yuli 2019, Majalisar wakilai ta yi kira ga ministirin ilimi ta gwamnatin tarayya da ta saka gwagwarmayar June 12 a cikin manhajar karatun tarihi a duka makarantu a fadin kasar nan.

Hakan ya biyo bayan amincewa da majalisar ta yi da wani kudiri mai suna “Bukatar a sanya gwagwarmayar June 12 cikin manhajar karatun tarihi a makarantun Najeriya” wanda dan majalisa Olumide Osoba ya gabatar.

Osoba ya ce “Majalisa na sane da cewa kwanan nan shugaba Buhari ya amince da June 12 a matsayin ranar dimukaradiyya. Muna sane da cewa kwata kwata babu zancen June 12 a cikin manhajar karatun tarihi a makarantun Najeriya saboda sauran gwamnatocin da suka gabata ba su amince da ranar ba.”

KARANTA WANNAN: An gano kayan asibiti a cikin gidan wani mutumi a Jihar Akwa Ibom

Osoba ya bayyana cewa in har ba a sanya gwagwarmayar cikin manhajar karatun tarihi a makarantu ba, to kananan yara masu tasowa ba za su fahimci mahimmancin ranar ba da irin gudunmuwar da gwagwarmayar ta bayar wajen ganin an dawo mulkin dimukaradiyya a cikin lardi na hudu.

Dan majalisar ya bayyana cewa akwai bukatar a cusa gwagwarmayar June 12 a cikin manhajar karatun tarihi saboda “Zai taimaki yara masu tasowa su samu bayani akan mahimmancin ta ga tarihin siyasar Najeriya.”

Da kakakin majalisar ya tambayi amincewar yan majalisan, mafi rinjaye daga cikinsu suka amsa cewa sun amince.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel