Wannan rashin imani da mai yayi kama: Wani mutumi ya yiwa matarsa yankan rago a gaban 'ya'yansu saboda taqi yarda ya kwanta da ita

Wannan rashin imani da mai yayi kama: Wani mutumi ya yiwa matarsa yankan rago a gaban 'ya'yansu saboda taqi yarda ya kwanta da ita

- Wani mutumi dan kasar Indonesia ya yiwa matarsa yankan rago akan idon dansu

- Mutumin ya yanka matar tasa ne bayan ya bukaci ya kwanta da ita taqi amincewa

- Sai dai kuma cikin ikon Allah matar bata mutu ba, yayin da shi kuma aka tura shi gidan yari na tsawon shekara 10

An cafke Wani mutumi da aka bayyana sunansa da Anton Nuryanto, dan shekara 37, a Tanjung Priok, dake arewacin Jakarta, a Indonesia, da laifin kai wa matarsa hari bayan taqi amincewa ya kwanta da ita.

A cewar hukumomin kasar, Anton yana kwance da matar tasa mai shekaru 34 da kuma karamin dansu, ranar Juma'a da misalin karfe 5 na Asuba, sai yake tambayar matar tasa cewa yana so ya kwanta da ita.

Matar taki amincewa da bukatar mijin nata, inda shi kuma Anton ya tashi ya dauko adda yayi mata yankan rago akan idon karamin dansun.

KU KARANTA: Naira ta kusa zama labari: Za'a fara amfani da kudin ECO nan da shekara 1 - Ouattara

"Yaron yayi shiru ne kawai ya kasa yin komai," shugaban hukumar 'yan sanda na Tanjung Priok ya bayyana hakan a gurin wani taron manema labarai a yau.

Cikin ikon Allah matar ba ta mutu ba har makwabta suka kawo musu dauki, inda shi kuma Anton ya ranta ana kare.

Daga baya an cafko Anton a kusa da gidansu, yayin da ita kuma matar aka kai wani babban asibiti domin ceto rayuwarta.

"Yanzu haka dai ta dawo hayyacinta har tana iya magana," in ji jami'in dan sandan.

An tisa keyar Anton zuwa gidan yari na tsawon shekara goma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel