Masu gudu su gudu: An kafa kwamitin da zai kwato kudaden gwamnati da aka sace

Masu gudu su gudu: An kafa kwamitin da zai kwato kudaden gwamnati da aka sace

- Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammeed Abdulkadir ya amince da nadin kwamitin mutum 17

- An nada kwamitin don su kwato duk wasu kudaden da aka cika ma yan kwangila dake aiki a jihar ba tare da ka’ida ba.

- Gwamnan ya baiwa kwamitin wata uku don su gudanar da binciken

A kokarinshi na ganin ya kwato kudade da kayayyakin gwamnati da aka sace, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammeed Abdulkadir ya amince da nadin kwamitin mutum 17 da tsohon sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya, sanata Isah Hamman Misau zai jagoranta.

A jawabin da mai magana da yawun gwamnan, Ladan Salihu ya fitar, kwamitin zai yi anfani da duk wata hanya don ganin an kwato duk wasu kudaden da aka cika ma yan kwangila dake aiki a jihar ba tare da ka’ida ba.

Haka zalika kwamitin zai tuntubi ma’aikatu da hukumomi na gwamnatin jihar don sanin gine ginen da gwamnatin jihar ta yi amma ta kyautar da su ga mutane daga May 2007 zuwa May 2019, don duba gaskiyar yadda aka rarraba gine gine da niyyar kwato ma gwamnati a inda aka rarrabasu ba a kan ka’ida ba.

Haka zalika wani alhakin da aka dora ma kwamitin shine su duba yadda gwamnatocin jihar tun daga May 2007 zuwa May 2019 suka raba filaye ba tare da bin ka’idar da kundin tsarin mulki da dokar filaye ta 1978 suka bayar ba.

Kwamitin zai kuma yi hadaka da komishinan shari’a na jihar don ganin yadda za a gurfanar da duk wanda a ka kama da laifin barnatar da kudin gwamnatin ko filaye da gine ginen gwamnati a gaban kuliya.

KARANTA WANNAN: Buhari ya aika ma majalisa sunayen mutane 15 da zai nadasu mukamin mashawarta

Sauran yan kwamitin sun hada da Umaru Bara’u Ningi, Keftin Tijjani Baba Gamawa, Alhaji Musa Gora, CP Hamisu Makama (rtd), Malam Musa Share, Alhaji Bibi Dogo, Kamal Isah, Haruna Gayuba, Barista Lawal Husaini Ibrahim, Alhaji Sani Shehu (Sanin Malam), Arc Bala Mohammed Dadi, Hon Maryam Garba Bagel, Janar Markus Yake (rtd), ACP Musa Konkyiel (rtd) da kuma Farfesa Sylvester Shagiyi (SAN) a matsayin sakataren kwamitin.

Gwamnan ya baiwa kwamitin wata uku don su gudanar da binciken su kuma kai mashi rahoto.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel