An sake kwatawa: Mutane 4 sun mutu a harin yan bindiga a jahar Taraba

An sake kwatawa: Mutane 4 sun mutu a harin yan bindiga a jahar Taraba

Wasu gungun yan bindiga sun kaddamar da hari a kauyen Murbai dake cikin karamar hukumar Ardo-Kola na jahar Taraba inda suka halaka mutane har lahira babu gaira babu dalili.

Rahoton gidan talabijin na Channels ya ruwaito wasu yan mata biyu da suka tsallake rijiya da baya a harin, Beauty Raphael da Mary Godfrey sun bayyana cewa yan bindigan sun shiga kauyen ne a ranar Laraba, 10 ga watan Yuli a kan babura.

KU KARANTA: Buhari ya aika ma majalisa sunayen mutane 15 da zai nadasu mukamin mashawarta

Beauty Raphael tace shigar yan bindigan keda wuya suka mamaye kauyen, kuma suka shiga harbe harbe irin na mai kan uwa da wabi, ita kuma a lokacin tana hanyar gona, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

“Mun tafi gona tare da kawayena mutum 6 da nufin sayo masara, amma yayin da muke kan hanya sai wasu yan bindiga suka taremu, suka zagayemu, daga nan suka bude mana wuta, ni ce a gabansu, Allah Ya kiyayeni harsashi bai sameni ba, amma na san mutane 4 sun mutu, ban san sauran ba.” Inji ta.

Ta kuwa Mary cewa ta yi daga cikin wadanda aka kashe akwai mata uku da namiji guda, kuma daga cikin matan akwai kanwarta wanda aka aiketa sayo itace don girkin abincin dare, haka zalika ta bayyana sunan namijin, Sani.

Yan matan sun ce ta cikin dazuka suka bi suka tsira, sa’annan sun tabbatar da cewar a yanzu haka gawarwakin wadanda aka kashe suna dakin ajiyan gawarwaki na cibiyar kiwon lafiya na gwamnatin tarayya.

Sai dai kaakakin rundunar Yansandan jahar Taraba, David Misal ya bayyana cewa har zuwa lokacin tattara wannan rahoton DPO na Yansandan Ardo-Kola bai basu rahoton harin ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel