An gano kayan asibiti a cikin gidan wani mutumi a Jihar Akwa Ibom

An gano kayan asibiti a cikin gidan wani mutumi a Jihar Akwa Ibom

Hukumar ICPC mai yaki da masu satar dukiyar gwamnati a Najeriya, ta bayyana cewa ta gano wani na’urar asibiti mai ‘dan-karen tsada a dankare a cikin wani gida a jihar Akwa Ibom.

Kamar yadda rahotonni su ka zo mana, ya kamata a ce wadannan kayan aikin duba lafiya su na cikin wani babban asibitin da ke Garin Ukana a cikin karamar Essien Udim na jihar Akwa Ibom.

Kayan aikin da a ka samu jami’an na hukumar ICPC su ka samu cikin wannan gida sun hada da na’urar da ke wanke koda da kuma kwalbar asibiti da a ke sa jariran da ba a ka haifa babu kwari.

Bayan haka kuma hukumar ta ICPC ta yi nasarar gano wasu manyan janareta har 2 masu karfin 15 KVA a cikin wannan gida. Kwamishinan ICPC na jihar watau Shola Shodipo ya bayyana wannan.

KU KARANTA: Wasu kayan wutan lantarki da a ka shigo da su cikin Najeriya sun yi dabo

Mista Shola Shodipo ya ke cewa ya kamata a kai wadannan kaya asibiti tun 2018, amma a ka karkatar da su zuwa cikin wannan gida a ka boye, sai dai yanzu an mika zuwa asibitin da ya dace.

Dakta Mary Udoh wanda ta karbi wadannan kayan aiki a madadin asibitin ta ji dadin wannan kokari da hukumar ta ICPC ta yi domin bunkasa lafiyar al’ummar wannan yanki na Ukama.

Kwamishinan na Hukumar ICPC ya ce za su yi bincike domin gano ainihin wanda ya boye wadannan manyan kayan aiki da a ka sayawa asibiti da sunan kwangilar Mazabu na ‘yan majalisa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel