Buhari ya aika ma majalisa sunayen mutane 15 da zai nadasu mukamin mashawarta

Buhari ya aika ma majalisa sunayen mutane 15 da zai nadasu mukamin mashawarta

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika ma majalisar dattawa sunayen mutane goma sha biyar da yake murdin nadasu matsayin wadanda zasu bashi shawarwari a fannoni daban daban, inji rahoton jaridar Sahara Reporters.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari ya aika ma majalisar sunayen ne a ranar Laraba, 10 ga watan Yuli, kamar yadda Mista Charles Akpan, mataimakin darakta a fadar shugaban kasa ya tabbatar.

KU KARANTA: Rukunin farko na maniyyata yan Najeriya 495 sun shilla Makkah daga Katsina

Mista Akpan yace “Sashi na 151 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya baiwa shugaban kasa daman ya nada masu bashi shawara wajen gudanar da ayyukansa, don haka shugaban kasa yake neman amincewar Sanatoci domin ya nada mashawarta 15.”

Ana sa ran shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan zai karanta ma takwarorinsa wasikar da shugaban kasa Buhari ya aiko masa dake kunshe da wannan bukata a zaman majalisar na ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli.

Sai dai har yanzu shugaban kasa bai aika ma majalisar dattawa sunayen sabbin ministocinsa ba sama da kwanaki 40 bayan rantsar dashi a matsayin shugaban kasa karo na biyu, hakan ya janyo cece kuce a tsakanin yan Najeriya.

Amma Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa watakila shugaban kasa ya aiko musu da sunayen mutanen da yake muradin nadawa mukaman ministoci kafin karshen wannan mako.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika ma majalisar dattawa sunayen wasu mutane guda 5 da yake muradin nadawa mukamin kwamishinoni a hukumar sadarwa ta kasa, NCC.

Buhari ya bayyana haka ne ciki wata wasika daya aika ma majalisar dake kunshe da sunayen mutanen da kuma mukamansu, inda ya nemi majalisar ta tantance mutanen kafin ya kai ga nadasu, kamar yadda tsarin mulki ya basu dama.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel