Muna matukar bukatar addu’o’inku a wannan lokaci– Buhari ga mahajjatan Najeriya

Muna matukar bukatar addu’o’inku a wannan lokaci– Buhari ga mahajjatan Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki maniyyata aikin Hajji daga Najeriya dasu taimaka ma kasar da kyawawan addu’o’in alheri a yayin zaman dasu yi a kasar mai tsarki.

Legit.ng ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi a filin sauka da tashin jirage na jahar Katsina lokacin da rukunin farko na maniyyatan Najeriya zasu tashi zuwa kasar Makkah a jahar Katsina a ranar Laraba, 10 ga watan Yuli.

KU KARANTA: Gwamnonin Najeriya sun bara, sun bukaci Buhari ya janye tallafin man fetir

Muna matukar bukatar addu’o’inku a wannan lokaci– Buhari ga mahajjatan Najeriya

Masari
Source: Facebook

Shugaban wanda ya samu wakilcin gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari ya gargadi jami’an hukumar kulawa da alhazai da su guji muzanta ma mahajattan Najeriya, kuma kada su yi sakaci da aikinsu.

Ya kara da cewa akwai bukatar jami’an hukumar alhazai su baiwa walwalar mahajjata fifiko yayin da suke gudanar da ibadar aikin Hajji, domin kuwa kasar Najeriya na bukatar addu’o’insu a wannan lokaci fiye da kowanni lokaci.

Buhari ya yi kira ga mahajjatan da su yi amfani da wannan daman wajen gyara alakarsu da Ubangiji Allah mai girma da daukaka ta hanyar gudanar da ibadojin daya kaisu, sa’annan su tabbata sun yi amfani da lokacinsu yadda ya kamata.

Shima jakadan kasar Saudiyya a Najeriya, Yusuf Al-Ghamdi ya shawarci maniyyatan dasu kauce ma shigar da miyagun kwayoyi kasar Saudiyya, kuma su kasance masu bin doka da oda a yayin zamansu a kasar.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk, shugaban hukumar alhazai ta kasa, Abdullahi Muktar, mataimakin kaakakin majalisar wakilai, Idris Wase, shugaban kungiyar Izala reshen jahar Katsina, Sheikh Yakubu Musa, shugaban kamfanin MaxAir Dahiru Mangal da sauran manyan jami’an gwamnatin jahar Katsina.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel