Dami guda na na’urorin jawo wutar lantarki sun bace – Inji Shugaban TCN

Dami guda na na’urorin jawo wutar lantarki sun bace – Inji Shugaban TCN

Wani labari mai ban mamaki ya zo mana inda mu ka ji kamfanin da ke da alhakin jawo wutar lantarki a Najeriya na TCN ta bayyana cewa ba ta ga wasu kaya da ta shigo da su kwanan nan ba.

Shugaban kamfanin TCN na kasa, Alhaji Usman Gur Muhammad Mohammed, ya fito ya bayyana cewa an samu wani daga cikin tarago 775 da su ka shigo da kayan wutan babu komai a cikinsa.

Usman Gur Mohammed ya bayyana wannan ne a babban birnin tarayya Abuja lokacin da ya zanta da Manema labarai. Gur Mohammed ya yi wannan jawabi ne Ranar 8 ga Watan Yuni, 2019.

Duk da haka dai shugaban na TCN ya bayyanawa Menama labaran cewa Najeriya za ta samu karfin wutan lantarki na akalla megawatt 2000 zuwa 3000 idan ta kara karfin wasu kayan aiki.

KU KARANTA: Wutar lantarki: Shehu Sani ya yi magana kan shirin binciken Obasanjo

Shugaban TCN din na Najeriya ya kuma bayyanawa ‘yan jarida cewa a halin yanzu kamfanin kasar ya cin ma matakin da a ke da bukata a yankin Nahiyar Afrika na karfin jawo wuta.

A jawabin da Mohammed ya yi, ya koka da cewa duk da kudin da a ka kashe a harkar jawo lantarki, kamfanonin da ke raba wuta ga jama’a sun ki sayen kayan aiki na zamani da su ka dace.

Alhaji Mohammed ya ce wannan ne ya ke jawo daukewar wutar da a ke samu a farat daya. Har ila yau, Mohammed ya ce shugaban kasa Buhari ya amince da shirin yi wa DisCos garambawul.

Gur Mohammed ya kuma fayyace shirin shigo da wasu manyan kayan aiki da za su karawa kasar megawatt 230 da zarar sun samu sa-hannun kamfanin da ke kula da sha’anin wuta na NERC.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel