Rukunin farko na maniyyata yan Najeriya 495 sun shilla Makkah daga Katsina

Rukunin farko na maniyyata yan Najeriya 495 sun shilla Makkah daga Katsina

A ranar Laraba, 10 ga watan Yuli ne jirgin farko na maniyyata aikin Hajji yan Najeriya ya tashi daga jahar Katsina dauke da mutane dari hudu da casa’in da biyar (495), kamar yadda hukumar aikin Hajji, NAHCON ta bayyana.

Legit.ng ta ruwaito maniyyatan sun hada da Mata 208, Maza 287 da kuma jami’an kula da mahajjata guda 20, inda suka daga filin sauka da tashin jiragen sama na tunawa da Umaru Musa Yar’adua da misalin karfe 7:10 na dare.

KU KARANTA: Atiku ya koka yawan bashin da Buhari ya ciyo ma Najeriya a shekara 4

Rukunin farko na maniyyata yan Najeriya 495 sun shilla Makkah daga Katsina

Rukunin farko na maniyyata yan Najeriya 495 sun shilla Makkah daga Katsina
Source: Facebook

Jirgin sama na kamfanin MaxAir mai lamba NGL3001 ne ya kwashi maniyyatan da suka fito daga Mani, Dutsanma da Kurfi, inda ya lula kasar Saudiyya, duba da tafiyan awanni 4.6 zai yi sama, ana sa ran zai isa Jidda da misalin karfe 12 na daren Alhamis.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga maniyyata aiki Hajji daga Najeriya dasu taimaka ma kasar da addu’o’i domin kuwa babu wani lokaci da Najeriya ke bukatar addu’o’insu kamar yanzu.

Haka zalika Buhari ya gargadi jami’an hukumar kulawa da alhazai da su guji muzanta ma mahajattan Najeriya, kuma kada su yi sakaci da aikinsu. Buhari ya bayyana haka ne ta bakin gwamnan jahar Katsina Aminu Bello Masari yayin tashin jirgin farko na mahajatta daga jahar Katsina a ranar Laraba.

Buhari ya yi kira ga mahajjatan da su yi amfani da wannan daman wajen gyara alakarsu da Ubangiji Allah mai girma da daukaka ta hanyar gudanar da ibadojin daya kaisu, sa’annan su tabbata sun yi amfani da lokacinsu yadda ya kamata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel