Gwamnonin Najeriya sun bara, sun bukaci Buhari ya janye tallafin man fetir

Gwamnonin Najeriya sun bara, sun bukaci Buhari ya janye tallafin man fetir

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari daya janye tallafin kudaden da gwamnati ke antayawa a harkar man fetir, domin kuwa ba abu bane mai daurewa, inji rahoton jaridar The Cables.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban kungiyar, gwamnan jahar Ekiti, Kayode Fayemi ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 10 ga watan Yuli yayin wata ziyara daya kai ma sabon shugaban NNPC, Mele Kyari, inda yace tallafin man fetir na karar da kudin Najeriya.

KU KARANTA: Atiku ya koka kan yawan bashin da Buhari ya ciyo ma Najeriya a shekara 4

Kayode ya cigaba da cewa tallafin man fetir ya mayar da hannun agogo baya a gwamnati, kuma ya zama tamkar wani adashin da babu kwasa musamman a wannan lokaci da kudaden shigar da gwamnati ke samu daga cinikin man fetir ke raguwa saboda karyewar darajar farashin danyen mai a kasuwan duniya.

“Wannan kira ya zama wajibi duba da raguwar kudaden shiga da gwamnati ke samu daga man fetir, da kuma karuwar bukatar da gwamnati ke dashi na kudade, mun tabbata a halin da ake ciki yanzu, kudin tallafin man fetir zai kwashe duk wani ribar da za’a samu daga cinikin man fetir.

“A shekarar 2016 da farashin gangar mai ya fadi warwas zuwa dala 48.11, kudin talafin man fetir bai wuce naira biliyan 28.6 ba, amma sun yi tashin gwauron zabi zuwa naira biliyan 219 a shekarar 2017, ya kara tashi zuwa biliyan 345 a 2018, ya kamata mu duba wannan lamarin domin yana shafan kokarin samar da wutar lantarki, tsaro da daidaiton tattalin arziki.” Inji shi.

Wannan kira da gwamnoni suka yi sun kara jaddada maganganun da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya yi ne a baya, da kuma wanda jakadan kasar Amurka, Stuart Symington ya yi game da bukatar janye tallafin mai, tare da yin amfani da kudaden wajen inganta ilimi, kiwon lafiya da kuma gina ababen more rayuwa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel