Majalisa za ta yi bincike kan yadda siyasa ya shiga harkar neman aiki

Majalisa za ta yi bincike kan yadda siyasa ya shiga harkar neman aiki

Mun ji cewa majalisar wakilan tarayya za ta gabatar da wani bincike na musamman a game da yadda a ke daukar sababbin ma’aikata a hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya na MDA.

Kamar yadda mu ka samu labari, an kafa wani kwamiti a majalisa da zai duba yadda siyasan addini da kabilanci ya shiga cikin harkar daukar sababbin ma’aikata a manyan hukumomi.

Majalisa ta na zargin cewa a na watsi da tsarin FCC wajen raba aiki a Najeriya. Honarabul Yusuf Gagdi mai wakiltar jihar Filato a karkashin APC ne ya kawo wannan magana a zauren majalisar.

KU KARANTA: Ka da ka kashe kasar nan da bashin hauka - Atiku ga Buhari

Majalisar ta yi na’am da wannan batu da Yusuf Gagdi ya kawo, kuma ta nemi nada kwamiti domin duba wadannan zargi na cewa a na la’akari da addini, kabilanci da siyasa kafin a ba mutane aiki.

Wannan kwamiti da a ka kafa jiya Laraba, 10 ga Watan Yuni, 2019 zai yi aiki ne a karkashin Hon. Wole Oke. A na sa rai nan da ‘yan kwanaki wannan kwamiti ya gabatar da rahotonsa a majalisar.

Majalisar ta kawo wannan magana ne domin ganin kowane ‘dan kasa ya samu damar shiga aikin gwamnati ba tare da nuna banbanci da sabanin siyasa, ko kuma ra’ayin addini da kabilanci ba.

Sashe na biyu na kundin tsarin mulkin Najeriya ya na goyon bayan a ba kowa damar cin romon arzikin kasarsa. Wannan ya sa a kawo dokar FCC domin gwamnati ta rika tafiya da kowa a kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel