Magudin jarabawa: Kwalejin Ibadan ta bankawa wayoyin salula na miliyoyin kudi wuta wanda ta karbe daga hannun dalibai

Magudin jarabawa: Kwalejin Ibadan ta bankawa wayoyin salula na miliyoyin kudi wuta wanda ta karbe daga hannun dalibai

- Hukumar gudanarwar Kwalejin fasaha da kere-kere ta Ibadan ta kona wayoyin miliyoyin kudi

- Mataimakin shugaban kwalejin ne ya shaida mana wannan labari inda yake cewa hukumar makarantar ta yanke shawarar kona wayoyin ne domin kawar da matsalar magudin jarabawa tsakanin dalibai

- Dokar rubuta jarabawar Kwalejinmu bata amince wa ko wane dalibi shiga da waya dakin jarabawa ba a cewar Oyeleke

Hukumar gudanarwar Kwalejin fasaha da kere-kere ta Ibadan ta jaddada kudurinta na kawar da magudin jarabawa a kwalejin ta hanyar amfani hukuncin mai tsaurin gaske.

Da yake jawabi ga manema labarai, Mataimakin shugaban kwalejin, Bayo Oyeleke a ranar Laraba ya ce, hukumar kwalejin ta riga da ta tsara yadda zata fatattaki lamarin magudin jarabawa a tsakanin daliban kwalejin.

A don haka, Oyeleke ya bayyana mana cewa, hukumar makarantar ta ba da umarnin kona wayoyin salula da aka karbe daga hannun dalibai a yayin gudanar da jarabawa, wadanda aka kone kurmus a harabar kwalejin ranar Laraba.

A cewar Oyeleke, wayoyin da aka karben daga hannu dalibai a lokacin jarabawa na miliyoyin kudi ne. Kuma hukumar zartarwar kwalejin ta yanke shawarar cewa a kona wayoyin ne domin daliban su fahimci cewa yaqi da magudin jarabawar da gaske ake yinsa

KU KARANTA: Rikicin ‘yan shi’a: Sufeto janar na ‘yan sanda ya ziyarci jami’an da aka raunana a Asibiti (Hotuna) .

Oyeleke ya cigaba da cewa: “ Manufarmu a nan ita ce mu tabbatar da mun yaye dalibai masu nagarta da kuma tarbiya, wadanda suka yi aiki tukuru domin samun kwalin makarantarmu, ba macuta ba.

“ Akwai dokokin makaranta dangane da rubuta jarabawa, duk dalibin da aka samu ya karya daya daga cikin dokokin tabbas zai dandana kudarsa. Daga cikin wadannan dokokin, babu dalibin da aka amince masa shiga da wayar salula dakin jarabawa.

“ Akwai shi a rubuce baro-baro cikin dokokinmu na rubuta jarabawa, wannan dalilin ne ya sanya muka dauki matakin kona wayoyin saboda nan gaba sauran daliban su kiyaye aikata aiki irin wannan.” A cewar Oyeleke.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel