Gwamna Emeka Ihedioha ya kawo tsarin asusun TSA a Jihar Imo

Gwamna Emeka Ihedioha ya kawo tsarin asusun TSA a Jihar Imo

Gwamnan Imo, Emeka Ihedioha, ya sa hannu a kan wata doka da za ta sa gwamnatin Imo ta koma amfani da tsarin asusun bai-daya a kaf fadin jihar kamar yadda gwamnatin tarayya ta yi a 2015.

A Ranar Laraba, 10 ga Watan Yuni, 2019, bayan kammala taron majalisar zartarwa, gwamnan na Imo ya tabbatar da cewa ya rattaba hannunsa a kan wannn doka mai cikakken iko da ya kawo.

Emeke Ihedioha ya bayyana wannan ne jim kadan bayan ya karbi wani rahoton tattalin arzikin jihar da Hadimansa su ka mika masa a taron mako-mako na Kwamishinoni da aka saba yi.

Gwamnan ya jagoranci wannan taron ne a gidan gwamnatin jihar Imo da ke cikin Garin Owerri a Ranar Laraba. Ihedioha ya koka da yadda Ma’aikatun jihar Imo ke yawo da kudin gwamnati.

KU KARANTA: Osinbajo ya yi wa sababbin Jami'an tsaron Najeriya huduba

A dalilin hada kan dukiyar gwamnati da kuma kudin da ke shigowa jihar ne gwamnan ya bada umarni duka Ma’aikatu da hukumomi su koma kan tsarin asusun na bai-daya watau TSA.

Bugu da kari, an haramtawa jami’an gwamnati karbar kudi hannu, inda ya umarci a nemi banki domin irin wannan hada-hada. Gwamnan ya na ganin wannan zai taimakawa tattalin jihar.

Daga cikin wadanda su ka halarci wannan taro da a ka yi a gidan gwamnatin, akwai manyan Jami’an gwamnati, jami’an tsaro, Sakatarorin din-din-din da kuma Sararkunan gargajiya na jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel