Cibiyar Arewa House za ta tsara laccar shekara-shekara domin koyi da Buhari - Idris Jimada

Cibiyar Arewa House za ta tsara laccar shekara-shekara domin koyi da Buhari - Idris Jimada

Mun ji cewa Cibiyar nan ta tarihin Arewa wanda a ke kira “Arewa House Centre for Historical Documentation and Research” ta bayyana shirin ta na karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wannan cibiya ta nemi ta rika shirya lacca duk shekara da nufin koyawa Duniya irin halin gaskiya da rikon amana da a ka san shugaban kasa Buhari da shi a shekarun da ya yi, ya na yi wa kasa hidima.

Fadar shugaban kasar ta bayyana wannan ne a cikin makon nan ta bakin Femi Adesina wanda ke magana da yawun shugaba Buhari. Adesina ya yi wannan jawabi ne a Ranar Talata, 9 ga Watan Yuni, 2019.

Mista Adesina ya ke cewa Darektan cibiyar ta Arewa House, Farfesa Idris Shaaba Jimada da jama'ar sa ne su ka kawowa shugaban kasar wannan ziyara inda ya fayyace masa wannan shiri da su ke yi.

KU KARANTA: Shugaba Buhari bai da ilmin da zai yi takara a Najeriya - Buba Galadima

A dalilin haka ne Darektan na cibiyar tarihin ya ke so a jefa irin wannan hali na shugaban kasar a cikin kwas din da a ke koyarwa a Makaranta. Cibiyar ta ce za ta so shugaba Buhari ya fara jan wannan ragama.

Idris Jimada ya fadawa shugaban kasar cewa akwai bukatar a cusawa jama’a irin dabi’arsa ta gaskiya da a ka san shi da shi tun ba yau ba. Jimada ya ce a na bukatar gaskiya wajen tafiyar da kasar nan.

A na sa jawabin, shugaba Buhari ya nemi Cibiyar ta dage wajen ilmantar yaran makaranta kan yadda za su rika yin gaskiya a cikin karatun da a ke koya masu kamar yadda a ka san Malamai a zamanin da.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel