AFCON: Buhari ya taya Super Eagles murnar samun nasara kan Afirka ta Kudu

AFCON: Buhari ya taya Super Eagles murnar samun nasara kan Afirka ta Kudu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles murnar samun nasara kan tawagar kungiyar kwallon kafa ta kasar Afrika Ta Kudu Bafana Bafana a gasar cin kofin Afrika (AFCON) da ake bugawa a kasar Masar.

Shugaban kasan ya bayyana gamsuwarsa kan irin bajinta da juriya da aiki tare da yan kungiyar Super Eagles din suka nuna a wasar.

Buhari ya aike da wannan sakon ne a shafinsa na sada zumunta na Twitter jim kadan bayan kammala wasar da aka buga a ranar 10 ga watan Yulin 2019.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Mutum 5 da suka mallaki arzikin da ya fi kasafin kudin Najeriya

"Ina taya Super Eagles murna kan nasarar da suka samu kan kasar Afrika Ta Kudu a daren yau. Tabbas kun nuna juriya da jarumta irin wadda aka san Najeriya da shi. Nasarori biyu suka rage kafin ku kawo mana kofin gida. Dukkan 'yan Najeriya suna fatan afkuwar hakan." inji Buhari.

Nasarar da Najeriya ta samu a wasar yau ya ba ta damar zuwa zagayen na kusa da karshe.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tawagar kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya ta samu nasara a kan tawagar Kamaru a gasar cin Kofin Kasashen Afirka na 2019 a kasar Masar wanda aka fafata a yammacin ranar Asabar, 6 ga watan Yuli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel