Wani asibiti a Kaduna ya koka bisa yadda 'yan sanda ke yawan kai ajiyar gawar mutane

Wani asibiti a Kaduna ya koka bisa yadda 'yan sanda ke yawan kai ajiyar gawar mutane

Hukumomin asibitin Yusuf Dantsoho da ke Tudun Wada a garin Kaduna sun bayyana damuwarsu a kan yawaita jibge gawar mutane da jami'an 'yan sanda ke yi a dakinsu na ajiye gawa ba tare da gabatar da kowacce irin takarda ba.

A wani bincike da Arewa Trust da ke fita duk karshen mako ta gudanar ya nuna cewa a cikin shekara guda jami'an 'yan sanda sun kai ajiyar gawa guda takwas asibitin ba kuma tare da sun kara waiwayarsu ba.

Jaridar ta gano cewa wani mai mukamin Saja daga ofishin 'yan sanda na Panteka ya kai ajiyar gawar wani mai suna Emmanuel, wanda ake zargin an kashe a kasuwar Panteka, a ranar 21 ga watan Yuli, 2017.

A ranar 28 ga watan Oktoba na shekarar 2018, an kai ajiyar gawar wani dan kasar Nijar mai suna Mustapha daga ofishin 'yan sanda na unguwar Kurmin Mashi.

Jaridar ta kara da cewa bincikenta ya nuna mata cewa a ranar 13 ga watan Nuwamba, 2018, wani jami'in dan sanda, Insifekta Abubakar Mohammed, na ofishin 'yan sanda da ke Kurmin Mashi, ya kai ajiyar gawar wani jariri mai kwana daya a duniya.

Insifekta Abdullahi Sani na ofishin 'yan sanda da ke Gidan Gayu ya kai ajiyar gawar wani mutum da ya yi ikirarin cewa kade shi aka yi da mota a ranar 8 ga watan Afrilu na shekarar 2019.

A ranar 23 ga watan Mayu na shekarar 2019, 'yan sanda sun kawo wani marar lafiya mai suna Ete Uyo, wanda daga baya ya mutu a asibitin amma har yanzu 'yan sanda basu sake waiwayensa ba.

Hakazalika, a ranar 5 ga watan Yuni, 2019, 'yan sanda daga ofishinsu da ke Rigasa sun kai ajiyar gawar wani da ake zargin me garkuwa da mutane ne.

A cewar wani ma'aikacin asibitin da bai yarda a ambaci sunasa ba, ya bayyana cewa: "a yawancin lokuta tilasta mana suke yi mu karbi gawar mutane da bamu sani ba kuma ba tare da sun kawo su da wata takarda ba, idan ma mun tambaye su sai su ce zasu kawo, daga nan ba zamu sake ganinsu ba.

"Haka wata gawar ke ajiye tun shekarar 2017 amma har yanzu basu kawo mana wata takarda da zata bamu damar rabuwa da gawar ba. Hasali ma, dan sandan da ya kawo gawar daga baya sai ya ce an yi masa canjin wurin aiki idan muka dame shi da kira a waya."

Da ya ke tabbatar da hakan, shugaban asibitin, Dakta Tijjani Fatai, ya ce gawarwakin sun zame wa asibitin alakakai.

Ya kara da cewa koda asibitin ya ki karbar gawar mutum, sai jami'an 'yan sanda su jibe ta a kofar dakin ajiyar gawa sannan su yi tafiyarsu abinsu.

Da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, sai ya dauki alkawarin cewa zai sake kira a waya bayan ya nemi karin bayani a kan lamarin amma har lokacin da aka wallafa rahoton bai sake kira.

Source: Legit

Mailfire view pixel