Yadda zanga-zangar mu a zauren majalisa ta rikide zuwa rikici - Kakakin 'yan Shi'a

Yadda zanga-zangar mu a zauren majalisa ta rikide zuwa rikici - Kakakin 'yan Shi'a

Kungiyar gwagwarmya ta 'yan uwa Musulmi da aka fi sani da 'Shi'a' ta musanta cewar ita ce silar barkewar rikicin da ya kai ga kwantar da jami'an 'yan sanda biyu yayin zanga-zangar da suka gudanar ranar Talata a zauren majalisa da ke Abuja.

A wani jawabi mai dauke da sa hannun Abdullahi Musa, kakakin 'yan Shi'a, kungiyar ta ce jami'an 'yan sanda suka kai hari a kan abokan aikinsu, ba mambobin Shi'a da ke zanga-zanga ba.

"Bayan sun aikata munanan abubuwa, 'yan sanda sun kewaye tare da kitsa labarin cewa mabiya Shi'a da ke zanga a zauren majalisa sun kwace bindiga daga hannun dan sanda tare da harbe shi. Wannan magana ba ta dace da hankali ba da kuma hujjoji na zahiri; abin ma ya zama wasa da hankalin mutane. Ta yaya mai zanga-zanga da bashi da makami zai iya kwace bindiga daga hannun jami'in tsaro har ya harba ta?

"Amma, idan aka yi la'akarai da kalaman kwamishinan 'yan sanda na Abuja, Sadiq Bello, a kan cewar rundunar 'yan sanda ta saka jami'anta a sirrance cikin masu zanga-zangar neman a saki Zakzaky, za a iya fahimtar cewa jami'an 'yan sandan da suka turo ne suka haddasa barkewar rikicin da ya faru a zauren majalisa yayin zanga-zangar mabiya Shi'a," a cewar jawabin.

DUBA WANNAN: Al'ada kowa ta irin ta sa: Dalilin da yasa mata masu dukiya ke auren mata 'yan uwansu a kasar Tanzania

Kakakin ya kara da cewa jami'an 'yan sandan Najeriya sun yi abubuwan da suka fi haka muni a tarinhinsu na aiki.

Da ya ke magana da jaridar Premium Times a ranar Laraba, Musa ya ce babu gaskiya a cikin rahoton rundunar 'yan sanda da ya bayyana cewa sun kama mambobin Shi'a 40, kazalika, ya bayyana cewa har yanzu basu ga mabiyansu fiye da 100 ba bayan rikicin da ya barke a ranar Talata.

Musa ya kara da cewa fiye da mambobin Shi'a 50 sun samu raunuka daban-daban.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel