KAI TSAYE: An tashi, Najeriya ta lallasa Afrika ta kudu

KAI TSAYE: An tashi, Najeriya ta lallasa Afrika ta kudu

Yayinda kofin Zakarun Afrika ke cigaba da gudana, Najeriya tana cikin karawa da kasar South Afrika a filin kwallon birnin Alkahira, babbar birnin kasar Misra.

Dan kwallon Najeriya, Chukwueze ya zirawa South Afrika kwallo daya min 27

A minti 75, dan kwallon South Afrika ya ramawa kasarsa

Ana saura minti biyu a tashi, dan kwallon Najeriya Chris Troost-Ekong ya zira kwallo daya mai ban haushi

Najeriya 2 - South Afrika 1

A yanzu haka, Najeriya za ta kara da duk wanda ya samu nasara tsakanin kasar Aljeriya da Kotdibuwa a wasan da za'a buga da yammacin Alhamis, 11 ga watan Yuli, 2019 da misalin karfe 5 bayan la'asar.

Hakazalika, kasar Senegal zata kara da duk wanda ya samu nasara a wasan Tunisiya da Madagascar da za'a buga a goben misalin karfe 8 na dare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel