Ruga: Kungiyar CAN ta nemi a kama mambobin kungiyar arewa

Ruga: Kungiyar CAN ta nemi a kama mambobin kungiyar arewa

Matasan kungiyar kiristocin Najeriya reshen kudu, tayi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, da yayi gaggawan kama mambobin kungiyar arewa, wanda suka bayar da wa’adin kwana 30 ga shugabannin kudu kan su amince da manufar Buhari na kafa Ruga.

Shugaban kungiyar ta YOWICAN, Oluchukwu Green Nnabugwu yayi Magana a Owerri inda ya kara da cewa Ruga ba zai magance matsalolin makiyaya ba.

Wata hujja da kungiyar ta matasan CAN ta bayar shine cewa ajandar kafa Ruga, kudiri ne na Musuluntar da kasar da kuma mayar da ita na Fulani.

Sun kara da cewa furucin kungiyar matasan arewan, na iya haddasa rabuwar kai a kasar, idan har ba a gargade su daga irin wadannan yunkuri ba.

Sai dai kuma kungiyar ta bayyana cewa ware fulotin kiwo shine hanyar da aka amince dashi a dubiya baki daya don kiwon dabbobi.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya amince da raba wa manyan makarantun Najeriya biliyan N5 domin gudanar da bincike

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Fadar shugaban kasa a ranar Talata, 9 ga watan Yuli, ta bayyana cewa ba a dakatar da shirin inganta lamarin dabbobi na kasa da Gwamnatin Tarayya ke son yi ba.

Yayin da take shawartan yan Najeriya kan cewa kada su damu da wa’adin kwana 30 da kungiyar arewa ta bayar akan shirin Ruga, fadar shugab kasa ta shawarci kungiyar da ta mutunta ofishin shugaban kasa wanda tace ta yake hukunci ne don ci gaban kasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel