Ku zage ku yi aiki, ba takama cikin kaki ba - Osinbajo ya gargadin sojojin Najeriya

Ku zage ku yi aiki, ba takama cikin kaki ba - Osinbajo ya gargadin sojojin Najeriya

A yayin da a ranar Laraba 10, ga watan Yulin 2019 aka gudanar da bincike yaye sabbin dakarun sojoji, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya yi masu kashedi a kan kare martabar kasar nan da rataya a wuyan su.

Yayin biki da kuma faretin yaye sabbin dakarun sojoji da aka gudanar a barikin sojin sama dake jihar Kaduna, mataimakin shugaban kasa ya yi masu kashedi akan kada su tsaya takama da kakin su ko kuma makamai da suka rika a madadin jajircewa wajen yiwa kasar nan hidima.

Osinbajo ya ce aikin damara musamman na sojoji ya kasance a mafi kololuwar mataki na yiwa kasa hidima da yake da bukatar matsanancin kishi, jajircewa da kuma gwarzantaka wajen bayar da kariya ga rayuka da kuma dukiyoyin al'ummar kasa.

Da yake jaddada kashedin sa a kan kada kakin da suka sanya ko makamai da za su rika su shashantar da su cikin takama, mataimakin shugaban kasar ya ce wajibi ne ga kowane dakarun soji ya fanshi kariyar kasar nan da rayuwar sa.

Ya kuma tunatar da sabbin dakarun a kan kalubalai na rashin tsaro dake addabar kasar nan a halin yanzu da suka hadar da ta'adar kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas, tirka-tirkar masu garkuwa da mutane da kuma tarzomar 'yan daban daji a wasu sassa na Najeriya.

KARANTA KUMA: Buhari ya yi alhinin mutuwar babban sojin sama, Hussani Abdullahi

A yayin ci gaba da gabatar da jawabai, Osinbajo ya yi tsokaci dangane da yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mike tsaye wurjanjan tare da gwamnonin jihohi wajen tumke damarar tabbatar da tsaro a fadin kasar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel