Da dumi-dumi: NJC ta amince wa Buhari nada Tanko a matsayin CJN mai cikakken iko

Da dumi-dumi: NJC ta amince wa Buhari nada Tanko a matsayin CJN mai cikakken iko

Majalisar Alkalai Ta Najeriya (NJC) ta bukaci Shugaba Muhamamdu Buhari ya tabbatar da Alkalin Alkalai na wucin gadi, Justice Tanko Muhammad a matsayin tabbatacen Alkalin Alkalai na kasa.

An cimma wannan matsayar ne yayin wata taron gaggawa da majalisar ta gudanar karkashin jagorancin tsohon Shugaban Kotun Daukaka Kara na Kasa, Justice Umaru Abdullahi.

A cikin jawabin da Direktan Yadda Labarai na NJC, Soji Oye ya fitar a ranar Laraba ya ce an cimma matsayar ne sakamakon rahoton da kwamitin da aka nada don tantance sabon alkalin alkalai na kasa ta gabatar da rahoton ta.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Mutum 5 da suka mallaki arzikin da ya fi kasafin kudin Najeriya

Sanarwar ta kuma ce kwamitin ta bawa gwamnatocin wasu jihohi shawarwarin nada wasu sabbin Shugabanin Alkalan Jihohi da Grand Khadis.

Jihohin sun hada da Lagos, Anambra, Ebonyi, Niger da Taraba; da kuma Grand Khadi a kotunnan Shari'a da ke jihohin Kano da Jigawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel