Masu maula ba Masana addini ba ne – Gwamna Sule ya yi tir da bara

Masu maula ba Masana addini ba ne – Gwamna Sule ya yi tir da bara

Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya yi barazanar ladabta Iyayen da su ke haihuwar ‘Ya ‘ya ba tare da daukar dawainiyarsu, inda a ke tura wasu yara yawon barace-barace.

Abdullahi Sule ya zari takobin maganin bara da wasu ke yi da sunan Almajiranci a yankin kasar. Gwamnan ya nuna sam wannan danyen aiki bai da wata alaka da koyon ilmin addinin Musulunci.

Mai girma gwamnan ya yi wannan jawabi ne lokacin da ya tattauna batun Almajiranci a gidan Talabijin na NTA na kasa, ya na mai bayyana ra’ayinsa. Gwamnan ya ce an jahilci wannan lamari.

Gwamna Sule ya bayyana cewa akwai Almajirai kusan miliyan 10 da ke yawo su na bara a jihohin Arewa, inda ya ce mafi yawan wadannan Almajirai sun zama ba su da abin yi sai yawon maula.

Injiniya Sule ya kuma yi magana a game da shirin nan na RUGA da gwamnatin kasar ta dakatar.

KU KARANTA: Gwamnan Gombe zai sa kafar wando daya da barayin Jiharsa

Gwamnan ya ke cewa: “An yi wa shirin RUGA da tsarin karatun Almajiranci mummunar fahimta, a zahiri su na kunshe da alheri, amma dole gwamnati ta yi watsi da shirin saboda jahilcin jama’a.”

Sule ya ke cewa a jihar sa ta Nasarawa, wannan bara da a ka saba ta zama wata ta fitina kuma babbar barazana ga sha’anin tsaro. Gwamnan ya ce yanzu ya kawo hanyar magance matsalar.

Daga cikin yadda gwamnatin Nasarawa za ta inganta tsaro, akwai neman kawo karshen bara ta hanyar tilastawa Iyaye daukar dawainiya. Sannan gwamnan ya ce zai koyawa Matasa sana’a da noma.

Har wa yau, gwamnan na APC ya ce akwai doka da za a kawo a jihar Nasarawa wanda za ta haramta barace-barace. Gwamnan ya ce dole a ba kananan yaran da a ke aikawa bara hakkinsu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel