Shugaba Buhari ya amince da raba wa manyan makarantun Najeriya biliyan N5 domin gudanar da bincike

Shugaba Buhari ya amince da raba wa manyan makarantun Najeriya biliyan N5 domin gudanar da bincike

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Laraba, ya amince kashe biliyan N5 a makarantun gaba da sakandire na kasa domin gudanar da bincike a bangarorn ilimi daban-daban.

Hukumar sarrafa kudaden gudanar da aiyuka a makarantun gaba sakandire (TETfund) ce za ta raba kudin ga manyan makarantun.

Babban sakataren hukumar TETFund, Farfesa Suleiman Bogoro, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin rantsar da wani kwamitin da zai gudanar da rabon kudin bayan ya tantance yadda za a raba su.

Farfesa Bogoro ya ce kudaden za su taimaka wa malamai a makarantun gaba da sakandire wajen gudanar da binciken da zasu kawowa kasa cigaba.

Ya bayyana cewa wanna shine kudi mafi tsoka da wata gwamnati ta taba ware wa TETFund domin gudanar da bincike tun bayan kafa hukumar a shekarar 2009.

Babban sakataren ya ce za a yi amfani da kudaden wajen gudanar da bincike a bangaren kimiyya, fasaha, kirkira, da wasu sauran bangarori da dama.

Farfesa Bogoro ya bayyana cewa an kafa kwamiti da ya kunshi tsofi kuma kwararrun malamai a manyan makarantu da zasu yi bitar takardun masu neman tallafi wajen gudanar da wani bincike domin zakulo wadanda suka cancanta a bawa kudi.

Ya bukaci mambobin kwamitin da su yi amfani da iliminsu da gogewa wajen zakulo takardun neman tallafi da suka fi dace wa a bawa tallafin.

A jawabinsa, shugaban kwamitin, Farfesa Olufemi Bamiro, ya dauki alkawari fara aiki ba tare da wani bata lokaci ba domin tabbatar da ganin cewa masu burin gudanar da bincike da ke neman tallafi sun samu damar cin moriyar kudaden domin samar da sakamakon da zai kawo wa kasa cigaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel