Buhari ya yi alhinin mutuwar babban sojin sama, Hussani Abdullahi

Buhari ya yi alhinin mutuwar babban sojin sama, Hussani Abdullahi

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya mika sakon sa na ta'aziyya tare da jajantawa iyalai, gwamnati da kuma al'ummar jihar Nasarawa biyo bayan babban rashin wani tsohon sojin sama, Vice Admiral Husaini Abdullahi mai ritaya.

Buhari cikin wani sako da ya gabatar da sanadin mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu, ya kuma jajantawa rundunar dakarun sojin Najeriya dangane da mutuwar tsohon gwamnan da ya jagoranci jihar Bendel a tsakanin watan Maris na 1976 zuwa watan Yulin 1978.

Da ya ke kwarara alhini a ranar Laraba 10 ga watan Yulin 2019, shugaban kasa Buhari ya yi waiwaye a kan rayuwar tsohon sojin da ya riga mu gidan gaskiya. Ya bayyana yadda rayuwar marigayi Hussain ta damalmale wajen yiwa kasar nan hidimi.

Kazalika shugaban kasar ya hikaito yadda tsohon sojin saman ya yi aiki tukuru wajen sauke nauyin da rataya a wuyan sa na hukumar sojin kasar nan tare da barin gadon kyawawan sawaye da dabi'u na koyi a yayin rayuwar sa.

Shugaban kasa Buhari ya yi rokon neman gafara ta neman Mai Duka ya jikan sa da rahama gami da kyautata masa makwanci. Ya kuma bayar da hakuri tare da neman Ubangijin Sammai da 'Kassai da bai wa Najeriya juriyar wannan rashi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel