Rikicin ‘yan shi’a: Sufeto janar na ‘yan sanda ya ziyarci jami’an da aka raunana a Asibiti (Hotuna)
-Sufeto janar na yan sanda ya ziyarci jami'an da suka samu rauni sakamakon gwabzawa da yan shi'a a Majalisar dokoki ranar Talata
-Sufeton ya shaidawa manema labarai cewa an riga da an damke mutum 40 daga cikin wadanda suka gudanar da wannan ta'asa
Sufeton janar na ‘yan sanda, Muhammad Adamu a ranar Laraba ya ziyarci Asbitin Kasa dake Abuja domin duba jami’ansa da suka samu rauni sakamakon karon battar da suka yi da ‘yan shi’a a Majalisar dokoki ranar Talata.

Asali: Twitter
KU KARANTA:Kotu tayi watsi da APC, ta tabbatar da Ishaku a matsayin gwamna
Jami’an sun samu rauni iri daban-daban a lokacin da ‘yan kungiyar shi’a mabiya Ibrahim El-Zakzaky suka kutsa cikin Majalisar dokokin a ranar Talata.

Asali: Twitter
A lokacin wannan ziyara,Sufeton ya bayyana ma ‘yan jarida cewa an riga an kama mutum 40 wadanda aka yi kutsen tare da su. Kuma a halin yanzu akwai jami’ai 5 wadanda ke karbar kulawa a cibiyar bayar da kulawa ta musamman dake asibitin.

Asali: Twitter
Ya kara da cewa, rundunar yan sanda zata biya dukkanin kudin magungunansu, kuma bincike na cigaba da gudana domi tabbatar da cewa an kama ilahirin wadanda keda sa hannu cikin aukuwar wannan lamari.

Asali: Twitter
Idan baku manta ba, a jiya ne a wani gungun ‘yan shi’a ya dira Majalisar dokoki inda suke zanga-zangar a saki jagoransu El-Zakzaky.

Asali: Twitter
Jami’an tsaro sunyi kokari hanasu shiga majalisar amma daga baya abin yafi karfinsu har suka samu suka shiga cikin wato harbar majalisar. An kona motoci da dama yayin da jami’an tsaro tara suka samu raunuka.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng