Tirkashi: Asirin wani mutumi da 'yan sanda suke nema ruwa ajallo ya tonu, bayan ya saki wata uwar tusa mai firgitarwa

Tirkashi: Asirin wani mutumi da 'yan sanda suke nema ruwa ajallo ya tonu, bayan ya saki wata uwar tusa mai firgitarwa

- Wani mutumi dan Missouri da jami'an tsaro suka biyo shi da niyyar kamashi, ya shiga hannu

- Mutumin ya shiga hannu ne bayan wata uwar tusa da ya saka a lokacin da yake boye a wani guri

- Karfin karar tusar mutumin ita ce ta bayyanawa jami'an tsaron gurin da mutumin yake boyewa, suka je suka kamo shi

Wani mutumi dan Missouri wanda jami'an tsaro suke nema ruwa a jallo ya shiga hannu, bayan asirinsa ya tonu lokacin da ya banka wata uwar tusa a maboyarsa.

A cewar ofishin 'yan sanda na Clay County, a cikin karshen satin nan, jami'an 'yan sanda suna neman mutumin ruwa ajallo, inda aka basu umarnin kamo shi a duk inda suka same shi.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Tarihin da Hausawa ke bayarwa na Bayajidda labarin Gizo da Koki ne - Farfesa Abdallah

Mutumin da ake neman ya samu maboya mai kyau ya boye a lokacin da 'yan sandan suka biyo shi, amma kuma ya saki wata uwar tusa mai karfi wacce tasa 'yan sandan da suke binsa suka gano maboyar ta sa.

A karshe dai jami'an 'yan sandan sun cafke suka tisa keyarsa zuwa ofishinsu dake Clay County.

Labarin ya bazu a duniya ne bayan da ofishin 'yan sandan suka mai da lamarin abin dariya, inda suka wallafa labarin a shafinsu na Facebook sannan suka yi masa alama kamar haka "#ItHappened", ma'ana 'Ta Faru'.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel