Babbar magana: Kotu ta aike wa IGP Adamu da DCP Kyari sammaci

Babbar magana: Kotu ta aike wa IGP Adamu da DCP Kyari sammaci

- Jastis Dorcas Agishi ta babbar kotun tarayya da ke Jos, jihar Filato, ta umarci shugaban rundunar 'yan sanda da Abba Kyari su bayyana a gabanta

- Alkaliyar kotun ta bukaci manyan jami'an 'yan sanda su gaggauta kawo mata wani mai laifi da suka kama tun watan Fabrairu

- Agishi ta tsayar da 25 ga watan satumba a matsayin ranar da IGP da Abba Kyari zasu bayyana a gaban ta

A ranar Laraba ne Jastis Dorcas Agishi ta babbar kotun tarayya da ke Jos, jihar Filato, ta umarci babban sifeton rundunar 'yan sanda na kasa (IGP), Mohammed Abubakar Adamu, da mataimakin kwamishinan 'yan sanda (DCP) na rundunar ko ta kwana (IRT), Abba Kyari, da su gurfana a gabanta ranar 25 ga watan Satumba domin su bayyana dalilin da zai hana kotun tuhumarsu da nuna raini.

Sammacin da kotun ta aike musu na zuwa ne kwanaki bakwai bayan manyan jami'an 'yan sandan sun gaza gabatar da wani mai lafi a gaban ta.

An kama mai laifin, Mr Nanpon Sambo, tun a cikin watan Fabrairu na shekarar 2019 amma har yanzu ba a gurfanar da shi a gaban kowacce kotu ba.

Agishi ta gindaya wa IGP Adamu da DCP Kyari sharadin cewa tilas su bayyana a gaban kotu a sabuwar ranar da ta ambata, 25 ga watan satumba.

DUBA WANNAN: Abokai 3 sun dura wa budurwa mai juna biyu ruwan omo don ta yi barin cikin da take dauke da shi

"IGP Adamu da Abba Kyari su kawo mai laifin wannan kotu domin a dauki bayanansa sannan su ajiye shi a gidan yari da ke nan Jos har zuwa lokacin da kotu za ta dawo daga hutu

"Sannan su bayyana a gaban wannan kotu a zaman da za ta yi a ranar 25 ga watan Satumba domin su yi bayanin dalilin da zai hana kotu tuhumarsu da nuna raini ta hanyar kin yin biyayya ga umarnin kotu da gan-gan," a cewar Jastis Agishi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel