Cutar kwalara ta kashe mutane 48 a kasar Kamaru

Cutar kwalara ta kashe mutane 48 a kasar Kamaru

Adadin rayukan mutane da suka salwanta a sanadiyar barkewar cutar kwalara wato amai da gudawa, sun kai kimanin 48 a Arewacin kasa Kamaru kamar yadda wani babban jami'i na ma'aikatar lafiya a kasar ya bayyana.

Arabo Saidou, ya ce daga watan Afrilun da ya gabata kawowa yanzu, rayukan mutane 48 sun salwanta cikin yankin Arewacin kasar inda a halin yanzu kimanin mutane 775 suka kamu da cutar.

Furucin da babban jami'in na lafiya ya gabatar a ranar Laraba 10 ga watan Yuli, ya ce rashin tsaftace muhalli da kuma abinci ke da alhakin dasa wannan muguwar annoba da ke yiwa mutanen kasar dauki dai-dai.

Kwararrun kiwon lafiya na kasar sun alakanta tsinkewar cutar da rashin tsaftaccen ruwan sha da ya zamto tamkar zinare a Arewacin Kamaru.

KARANTA KUMA: Buhari zai kaddamar da gidauniyar wani asibitin ido na kasar Indiya a Abuja

A ranar Litinin da ta gabata, ministan lafiya na kasar Kamaru, Manaodu Malachie, ya bayyana rashin jin dadin sa tare da damuwa. Ya gargadi al'ummar kasar a kan kada yawan adadin su ya sanya su juya baya wajen tabbatar da tsaftar muhalli.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, tsawon shekaru aru-aru cutar kwalera ta ci gaba da kasancewa mafi munin annoba dake addabar kasar a sanadiyar ambaliyar da ta fi kamari musamman a lokutan damina.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel