Caine 2019: Shugaba Buhari ya aikawa Lesley Arimah sakon taya murna

Caine 2019: Shugaba Buhari ya aikawa Lesley Arimah sakon taya murna

Labari ya zo mana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito ya taya wanda ta lashe gasar adabin Afrikan nan wanda a ka saba yi duk shekara watau “Caine Prize for African Writing.”

Shugaban kasar na Najeriya ya aika sakon murnarsa ga wannan Baiwar Allah, Lesley Nneka Arimah wanda rubuce-rubucen ta, su ka sa ta zama gwarzon gasar da a ka yi a shekarar ta 2019.

Muhammadu Buhari ya yi wannan jawabi ne ta bakin babban Hadiminsa Femi Adesina wanda ke taimaka masa wajen harkokin yada labarai. Shugaban kasar ya jinjinawa basirar Lesley Arimah.

KU KARANTA: Majalisa ta nemi Shugaba Buhari ya nada Ministocinsa

A cewar shugaban kasar, Lesley Arimah, ta nuna bajinta wajen iya zakulo abubuwan da su ka shafi mata a rubutunta da tayi mai suna ‘Skinned’, inda ta taba abin da ke yi wa Duniya kaikayi.

Buhari ya ce akwai bukatar gwamnati ta maida hankali a kan wannan littafi da ‘Yar kasar ta sa ta rubuta mai kunshe da bayani na musamman a kan yadda za a karfafawa ‘Ya ‘ya mata a Afrika.

Ta bakin Adesina, Buhari ya taya dangin Marubuciyar murnar samun wannan gagarumar nasara, wanda a cewarsa ya kara tabbatarwa Duniya Baiwar ta, tare da yi wa Najeriya abin alfahari.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel