Yanzu Yanzu: Yan shi’a sun sake gagarumin zanga-zanga a Abuja, sun ce sun shirya mutuwa

Yanzu Yanzu: Yan shi’a sun sake gagarumin zanga-zanga a Abuja, sun ce sun shirya mutuwa

Wasu yan shi’a a ranar Laraba, 10 ga watan Yuli sun sake gudanar da zanga-zanga a Abuja,sun sha alwashin mutuwa don tsiratar da addininsu.

Masu zanga-zangan sun yi gangami daga hukumar kare hakkin dan adam da ke Maitama suka billa ta Transcorp Hilton har zuwa unguwar Gana, suna ta wakokin da suka saba ma gwamnati don kira ga a saki shugabansu, Ibraheem El-Zakzaky.

Sai dai kuma, sun bijirewa jami’an tsaro da ke sintiri a birnin a kokarinsu na neman kungiyar.

Shugaban masu zanga-zangar, Abdullahi Musa, yace matakin da gubar da ke jinin El-Zakzaky kamar yadda likitocinsa suka bayyana ya kai milligram 201.7 wanda ya kasance babban barazana ga lafiyarsa.

Yanzu Yanzu: Yan shi’a sun sake gagarumin zanga-zanga a Abuja, sun ce sun shirya mutuwa

Yanzu Yanzu: Yan shi’a sun sake gagarumin zanga-zanga a Abuja, sun ce sun shirya mutuwa
Source: UGC

“Rayuwarsa na cikin hatsari sannan babu dalilin da zai sa mu komawa gida mu zauna. A kullun masu zalunci na cin zarafin mu, suna sanya tsoro a zukatan mutane. Mun shirya mutuwa a wannan yanayi sannan kuma mun ce sai mun zo su shirya. Idan sun so su zo su kashe mu,” inji Musa.

KU KARANTA KUMA: Ku yiwa Buhari addu’an samun nasara – Shugabannin APC sun roki yan Najeriya

Ya karyata zargin ewa mambobin kungiyar sun harbi jami’an yan sanda biyu da kuma kona motoci 50 a harabar majalisar dokokin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel