Wata jam'iyyar adawa ta nemi janye karar kalubalantar zaben Buhari

Wata jam'iyyar adawa ta nemi janye karar kalubalantar zaben Buhari

Jam'iyyar People’s Democratic Movement (PDM) ta gabatarwa kotu bukatar ta na janye karar dan takarar shugaban kasar ta ya shigar kan Shugban Kasa Muhammadu Buhari, jam'iyyar APC da INEC.

Jam'iyyar PDM da dan takarar shugabancin kasar ta, Aminci Abu sun shigar da karar inda suke kallubalantar rashin sanya sunan jam'iyyarsu da dan takararta a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu.

An shigar da karar ne a karkashin sashi na 138 na Dokar Zabe da ya ce za a soke zabe duk lokacin da aka ware dan takarar da jam'iyyarsa ta zabe shi kan ka'ida amma ba a sanya sunansa cikin masu takarar zabe ba.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Mutum 5 da suka mallaki arzikin da ya fi kasafin kudin Najeriya

Barrister Aliyu Lemu ne ya wakilci Aminchi a kotu zaben a ranar Laraba yayin da Barrista Morrison Onunu ya wakilci jam'iyyar PDM wadda ta samu wakilcin shugaban ta na kasa Cif Frank Igwebuike.

Daily Trust ta ruwaito cewa takardan da PDM ta gabatarwa kotu ya kunshi abubuwa biyu; na farko shine janyewar PDM daga karar baki daya; na biyu kuma cire sunnan jam'iyyar PDP cikin jerin sunayen wadanda suka kallubalantar zaben.

Kotun sauraran kararrakin zaben ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 18 ga watan Yuli da kuma cigaba da sauraron wasu battuwan da suka shafi zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel