Buhari zai kaddamar da gidauniyar wani asibitin ido na kasar Indiya a Abuja

Buhari zai kaddamar da gidauniyar wani asibitin ido na kasar Indiya a Abuja

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis 11, ga watan Yuli, zai jagoranci kaddamar da gidauniyar TCF, Tulsi Chanrai Foundation na wani babban asibitin Ido a garin Abuja.

Babban asibitin wanda ke karkashin kulawar wata cibiyar ido ta Aravind Eye Care System dake kasar Indiya, na ci gaba da taka rawar gani da yin zarra a fagen lafiyar idanu cikin kasar nan a sanadiyar gudanarwar zakakuran likitocin idanu 30 'yan asalin Najeriya bayan samun kwarewa mai zurfi a kasar Indiya.

Da yake ganawa da manema labarai a garin Abuja, shugaban gidauniyar TCF, Dakta Jagdish Charai, ya ce a halin yanzu Asibitin zai ci gaba da gudanar da kaso 60 cikin 100 na harkokin duban lafiya kyauta domin kawo sauki da kuma rangwami musamman ga masu karamin karfi.

Asibitin da ya fara aiki gadan-gadan a watan Janairu na wannan shekara, ya duba lafiyar idanun fiye da mutane 6,400 yayin da aka yiwa mutane 1000 tiyatar idanu. An yiwa mutane kimanin 850 tiyatar idanu kyauta domin yunkurin yaye tazarar dake tsakanin talaka da masu hannu da shuni.

KARANTA KUMA: Yanzu wadanda aka yi garkuwa dasu na kubuta babu kudin fansa a Zamfara - Gwamna Mutawalle

A cewar babban Likitan, a halin yanzu asibitin ya yi kafuwar da zai iya samun ikon gudanar da tiyatar idanu 15,000 daban daban cikin kowace shekara.

A wani rahoton na daban da jaridar Legit.ng ta ruwaito, shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan, ya ce akwai yiwuwar shugaban kasa Buhari zai gabatar da sunayen ministocin sa gabanin karshen wannan mako.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel