Fayemi ya dauki wanda su ka gama karatun Likita aiki a Ekiti

Fayemi ya dauki wanda su ka gama karatun Likita aiki a Ekiti

Duka Dalibai 50 da su ke jami’ar jihar Ekiti da ke Garin Ado Ekiti, sun samu aiki kai-tsaye daga hannun gwamnatin jihar. Mun samu wannan labari ne a Ranar Laraba 10 ga Watan Yuni, 2019.

Kamar yadda labari ya zo mana daga gwamnatin jihar Ekiti, gwamna Kayode Fayemi ya zabi wadanda su ka gama karatun su yi aiki a jihar ne domin dawo da tsohuwar martabar ilmi a Ekiti.

Gwamnan ya sanar da daukar wannan aiki ne ta bakin babban Sakatarensa na yada labarai, Olayinka Oyebode a Ranar Talata. Oyebode ya ce gwamnatin jihar ta sakawa daliban ne da alheri.

Sakataren gwamnan ya kuma bayyana cewa wannan sanarwa ta zo ne a daidai lokacin da a ke radi-radin cewa gwamnatin Fayemi ta ba wani Hazikin dalibin jami’ar kyautar da ba ta kai ko ina ba.

KU KARANTA: Gidauniyar Kwankwasiyya za ta aika yara karatu zuwa Indiya

Gwamnatin Kayode Fayemi ta kuma bayyana cewa ta zabi daliban da su ka kammala karatun Digiri da matakin farko, ta aika su zuwa kasar waje domin karo ilmi inji Mista Olayinka Oyebode.

Bayan karyata labarin bada karamar kyauta ga Dalibin da ya yi zarra a jami’ar ta Ado Ekiti, gwamnatin jihar ta ce ta ba masu karantar ilmin shari’a da wasu bangarori gudumuwar karatu.

A cewar Oyebode, wannan duk ya na cikin shirin wannan gwamnati mai-ci na habaka ilmi wanda tuni martabarsa ta zube a fadin jihar, tare da yabawa wadanda su ka yi abin kirki a fanninsu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel