Shugaban kasa yayi kira ga mata da su hayayyafa don a bunkasa tattalin arzikin kasa

Shugaban kasa yayi kira ga mata da su hayayyafa don a bunkasa tattalin arzikin kasa

-Shugaban kasa John Magufuli na kasar Tanzania yayi kira ga matan kasar da su yi ta haihuwa ratata

-Ya bayyana cewa yawan mutane ne hanya mafi sauri wajen habbaka tattalin arzikin kasa

-Magufuli ya yi misali da Indiya da Najeriya a matsayin kasashe da suka ci gaba saboda yawan mutanensu

Shugaban kasa John Magufuli na kasar Tanzania yayi kira ga matan kasar da “Saki mahaifarsu” su haifi yara da yawa saboda ta wannan hanyar ne za a bunkasa tattalin arzikin kasa.

Ya bayyana cewa “Idan kasa na da yawan mutane, to za ta habbaka tattalin arzikinta. Shi ya sanya kasar China take da tattalin arziki mai karfi.” Ya kuma yi misali da kasar Indiya da kasar Najeriya a matsayin kasashen da suka bunkasa sandiyyar yawan mutanensu.

Ya kara da cewa “Nasan wadanda ke so su juya mahaifarsu za su yi Allah wadai da wannan kiran nawa. Ku saki mahaifarku, ku kyalesu can su juya ta su." Ya bayyana ma taron mutane a mahaifarshi ta garin Chato.

Tun cikin shekarar 2015 da ya karbi ragamar mulkin kasar, ya fara gangamin inganta tattalin arzikin kasar Tanzania, wanda hakan kuma ya taimaka tattalin arzikin ke habbaka da kashi shida zuwa bakwai cikin dari a kowacce shekara.

Amma ya bayyana cewa yawan haihuwa zai sanya tattalin arzikin kasar ya habbaka da sauri. A yanzu haka dai kasar da take a gabashin Afirika na da yawan mutane da ya kai miliyan 55, kuma ta na daya daga cikin kasashen duniya da aka fi haihuwa, inda duk mace guda ke haihuwar akalla yara biyar.

KARANTA WANNAN: Ku yiwa Buhari addu’an samun nasara – Shugabannin APC sun roki yan Najeriya

A cikin shekarar 2018, Magufuli ya bayyana cewa “Takaita haihuwa na raggwaye ne wadanda basu iya daukar dawainiyar ‘ya’yansu”. Sa’annan kuma ministirin lafiya ta kasar ta dakatar da tallar takaita haihuwa da kasar Amurika ke daukar nauyi.

Shugabannin yan adawa na kasar Tanzania sunyi Allah wadai da kiran Magufuli, inda suka bayyana cewa a yanzu ma yawan yan kasar matsala ne. Wasu na ganin cewa yawan zai kara tsananin talaucin da ake fama dashi a kasar.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel