Lawan ya bukaci a hukunta yan shi’a da suka kai hari majalisa

Lawan ya bukaci a hukunta yan shi’a da suka kai hari majalisa

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Lawan, yayi Allah wadai da harin da mambobin kugiyar shi’a da ke zanga-zanga suka kai majalisar dokokin kasar.

Lawan, wanda ya ziyarci wasu daga cikin jami’an yan sandan da ke jinya a yanzu haka a asibitin majalisar, ya samu rakiyar wasu sanatoci.

Yayinda yake alhini da mutanen da harin ya cika da su tare da yi masu fatan samun lafiya, Lawan yayi kira ga a hukunta wadanda ke da hannu a harin da aka kai majalisar.

KU KARANTA KUMA: Ku yiwa Buhari addu’an samun nasara – Shugabannin APC sun roki yan Najeriya

Lawan ya bukaci a hukunta yan shi’a da suka kai hari majalisa

Lawan ya bukaci a hukunta yan shi’a da suka kai hari majalisa
Source: Twitter

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shahararren malamin addinin Musuluncin nan da yayi kaurin suna wajen sukan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ahmad Gumi ya fara bin manya a Najeriya domin su sanya baki tare da kira ga shugaban kasa ya saki shugaban yan shia, Ibrahim Zakzaky.

Gumi ya yi wannan yunkuri ne duba da tarzomar da cigaba da rike shugaban yan shia, Ibrahim Zakzaky ke janyowa a babban birnin tarayya Abuja, da kuma gudun abinda ka iya faruwa a Najeriya gaba daya idan har gwamnati ta cigaba da rikeshi.

Jaridar Desert Herald ta ruwaito a kokarin ganin an shawo kan matsalar ne Sheikh Ahmad Gumi ya yi takanas ta Kano zuwa gidan jagoran APC, Sanata Ahmad Bola Tinubu, inda ya samu ganawa dashi, tare da yi masa magiya a kan ya yi ma Buhari magana don ya sako El-Zakzaky.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel