Yan bindiga sunyi awon gaba da babban sakataren Adamawa

Yan bindiga sunyi awon gaba da babban sakataren Adamawa

-Masu garkuwa da mutane sunyi awon gaba da babban sakataren ministirin albarkatun kasa na jihar Adamawa, Emmanuel Pindimso.

-Rundunar yan sanda ta jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin

-Iyalan sakataren sun bayyana cewa masu garkuwa da mutanen basu tuntube su ba

Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da cewa an yi awon gaba da babban sakataren ministirin albarkatun kasa na jihar Adamawa, Emmanuel Pindimso.

Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, jami'in hulda da jama’a na rundunar yan sanda ta jihar, DSP Sulaiman Nguroje, ya bayyana cewa an tura yan sandan babban sifeton yan sanda na musamman don ceto babban sakataren, sa’annan kuma a kama wadanda suka sace shi.

Ya bayyana cewa, an sace Pindimso a gidanshi dake a Clerk Quarters da misalin karfe 3:00 na dare kafin safiyar yau Laraba 10 ga watan Yuli 2019.

Ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun haura ta katanga suka shiga gidan suka dauke shi sa’annan suka shiga motar babban sakataren suka fita ta kofar gidan suka wuce dashi inda suka boye shi.

KARANTA WANNAN: Ku yiwa Buhari addu’an samun nasara – Shugabannin APC sun roki yan Najeriya

Wani daga cikin iyalan sakataren wanda yake a gidan a lokacin da aka yi awon gaba da sakataren, ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun shiga gidan da misalin karfe 3:20 na dare dauke da bindigogi.

Ya bayyana cewa “Sun kwace wayar shi da ta matar shi. Munyi kokarin samun shi ta waya amma basu daukar kiran.”

Har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoton, iyalan Pindimso sun ce wadanda sukayi garkuwan dashi basu tuntube su ba ballantana su fadi kudin da za a fanshe shi.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel