Garkame Zakzaky: Sheikh Ahmad Gumi ya kai ma Bola Tinubu ziyara don shawo kan Buhari

Garkame Zakzaky: Sheikh Ahmad Gumi ya kai ma Bola Tinubu ziyara don shawo kan Buhari

Shahararren malamin addinin Musuluncin nan da yayi kaurin suna wajen sukan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ahmad Gumi ya fara bin manya a Najeriya domin su sanya baki tare da kira ga shugaban kasa ya saki shugaban yan shia, Ibrahim Zakzaky.

Gumi ya yi wannan yunkuri ne duba da tarzomar da cigaba da rike shugaban yan shia, Ibrahim Zakzaky ke janyowa a babban birnin tarayya Abuja, da kuma gudun abinda ka iya faruwa a Najeriya gaba daya idan har gwamnati ta cigaba da rikeshi.

KU KARANTA: Matsalolin ma’aurata: Yadda wata mata ta kashe mijinta da budurwarsa a Legas

Jaridar Desert Herald ta ruwaito a kokarin ganin an shawo kan matsalar ne Sheikh Ahmad Gumi ya yi takanas ta Kano zuwa gidan jagoran APC, Sanata Ahmad Bola Tinubu, inda ya samu ganawa dashi, tare da yi masa magiya a kan ya yi ma Buhari magana don ya sako El-Zakzaky.

A yayin zaman tattaunawa, Gumi ya nanata ma Tinubu matsalolin da ka iya faruwa idan har gwamnatin Buhari ta cigaba da rike Zakzaky duk da rashin lafiyar da yake fama dashi, ga shi kuma wasu kotuna sun bada umarnin a sakeshi.

Majiyarmu ta ruwaito bayan sauraron jawabin malamin, sai Tinubu ya bashi tabbaci tare da alkawarin zai isar da sakonsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari. Baya ga Gumi, shima babban malamin darikar Tijjaniyyah, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi irin wannan kira a baya ga Buhari.

Wannan zama mai muhimmanci da Gumi ya yi da Tinubu ya tabbata ne ta hannun tsohon shugaban EFCC, Nuhu Ribadu, wanda shi ne ya hada wannan ganawar sirri tsakanin shuwagabannin biyu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel