Yanzu wadanda aka yi garkuwa dasu na kubuta babu kudin fansa a Zamfara - Gwamna Mutawalle

Yanzu wadanda aka yi garkuwa dasu na kubuta babu kudin fansa a Zamfara - Gwamna Mutawalle

A halin yanzu wadanda aka yi garkuwa da su a jihar Zamfara na kubuta daga hannun 'yan daban daji bisa ga ra'ayi kuma cikin ruwan sanyi ba tare da karbar wasu kudaden fansa ba kamar yadda gwamnan jihar Bello Matawalle ya bayyana.

Gwamna Matawalle ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa da sa hannun mai magana da yawun fadar gwamnatin sa, Alhaji Yusuf Idris, yayin ganawa da manema labarai a ranar Laraba 10 ga watan Yuli cikin birnin Gusau.

Hakan ta kasance a sakamakon shirin tabbatar da sulhu da gwamnan ya shimfida makonni uku da suka gabata a tsakanin 'yan daban daji da kuma sauran masu aikata ta'addanci na neman su da ajiye makamai domin wanzar da zaman lafiya a jihar.

A yayin da ake samun ci gaban da tasirin wannan yunkuri, gwamna Matawalle a ranar Talatar da gabata ya karbi bakuncin mutane takwas da kwamishinan 'yan sandan jihar, Usman Nagogo, ya jagoranci fansar su cikin ruwan sanyi gami da farin ciki.

Da yake bayyana farin cikin sa tare da yabawa shugaban jami'an 'yan sanda na jihar, gwamna Matawalle ya kuma bayar da umurnin gaggauta duban lafiyar mutanen takwas da suka kubuta a asibitin fadar sa dake kan hanyar Gada Biyu a birnin Gusau.

Babban jami'in na 'yan sanda ya ce mutane da kubutu sun hadar da Mata uku, da kuma kananan yara sun afka tarkon masu ta'adar garkuwa da mutane kimanin watanni hudu da suka gabata garin Dansadau dake karkashin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

KARANTA KUMA: Gwamna Bello ya karbi takardar neman izinin takarar gwamnan jihar Kogi

Kamar yadda kwamishinan 'yan sandan ya bayar da shaida, a halin yanzu akwai kimanin mutane 56 da suka kubuta a makon da ya gabata kadai a sakamakon shirin tabbatar sulhu da gwamna Matawalle ya shimfida.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, cikin tsawon shekaru tara da suka gabata, jihar Zamfara ta kasance cikin halin ni 'ya su a sanadiyar ta'adar garkuwa da mutane, 'yan daban daji, satar shanu, kone-konen gonaki da gidaje da kuma dukiyoyin al'umma.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel